NSCDC ta horas da jami’an tsaro masu zaman kansu domin inganta tsaro a Gombe

An tunatar da sabbin ma’aikatan tsaron cewa, fannin tsaro na masu zaman kansu na buƙatar jarumta da amana..

NSCDC ta horas da jami’an tsaro masu zaman kansu domin inganta tsaro a Gombe

A ƙoƙarinta na inganta ƙwarewa da tabbatar da tsayuwar daka a fannin tsaro masu zaman kansu, Hukumar tsaro ta Civil Defence (NSCDC) a Jihar Gombe ta horas da ma’aikatan tsaro masu zaman kansu guda 55 daga kamfanoni guda tara.

An gudanar da horarwar ne ta ɓangaren sashen kula da Kamfanonin Tsaro Masu Zaman Kansu (PGC), wanda ya samu halartar ma’aikatan tsaro daga kamfanoni kamar haka:

A. Kolo Security Guard Ltd, Ampu Security Guard Ltd, Silɓer Guard Security Ltd, Jewel Security Guard Ltd, Hardawa Security Guard Ltd, Pana Global Security Ltd, Arksego Security Ltd, Kombat Security Ltd, da Kings Guard Security Ltd.

A sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na Hukumar NSCDC, SC Buhari Sa’ad ya fitar, Kwamandan hukumar Gyama Gyawiya, ya bayyana muhimmiyar rawar da NSCDC ke takawa wajen bayar da lasisi, duba da kula da ayyukan kamfanonin tsaro masu zaman kansu a Nijeriya, kamar yadda dokar NSCDC ta shekarar 2003 da kuma ta 2007 suka tanadar.

Kwamandan ya tunatar da sabbin ma’aikatan tsaron cewa, fannin tsaron masu zaman kansu na buƙatar jarumta, amana da cikakken alhaki.

Ya buƙace su da su kiyaye ƙa’idojin aiki, su zama masu tsayayyen ɗabi’a da bin dokoki tare da mutunta haƙƙin ɗan adam a kowane hali.

Gyawiya, ya ƙara da cewa yadda suke gudanar da aikinsu zai zama madubin dubawa ga dukkan fannin tsaron masu zaman kansu. Inda ya buƙace su da su kasance abin koyi ta hanyar nuna ƙwazo, aminci da jajircewa a aikinsu domin su zama wakilai nagari a fannin tsaro masu zaman kansu.