NSCDC ta kama mutum 4 kan zargin fataucin yara a Oyo

An ceto mutane tara da suka haɗa da ƙananan yara biyu a wani otal da ke Apete a birnin Ibadan.

NSCDC ta kama mutum 4 kan zargin fataucin yara a Oyo

Hukumar tsaro ta sibil difens a Nijeriya (NSCDC) ta cafke wasu mutane huɗu da ake zargi da safarar yara mata da ƙananan yara domin yin karuwanci a Jihar Oyo.

Waɗanda ake zargin sun haɗa da: Joy Ben da Blessing Edet da Rose Michael da Okechukwu Michael.

Kwamandan NSCDC na jihar ta Oyo, Augustine Padonu ya ce an kama su ne a ranar 6 ga watan Agusta lokacin da aka ceto mutane tara da suka haɗa da ƙananan yara biyu a wani otal da ke Apete a birnin Ibadan.

Padonu ya kuma ce rundunar a wani samame na daban ta bankaɗo wani ɓoyayyen wurin fasaƙwaurin man fetur a wani daji da ke kusa da titin Gwagwasu Moore a yankin Kishi na Ibadan.

Ya kuma tabbatar da cewa ana ci gaba da ƙoƙarin cafke waɗanda ake zargin da aikata laifin.

Padanu ya ce, za a gurfanar da waɗanda ake zargi da laifin safarar mutanen a gaban kotu bayan kammala bincike.

Tags