Ntaganda ya gurfana a gaban Kotun Duniya
Tsohon dan tawayen kasar Congo, Mista Bosco Ntaganda, ya gurfana a gaban Kotun Duniya (ICC) mai hukunta laifuffukan yaki, inda ya ce ba ya da laifi a kan tuhumar da kotun ke masa ta laifufukan yaki.Kotun, wacce ke birnin Hague, tana tuhumar Ntaganda ne da aikata laifuffukan yaki 18, cikinsu har da kisan kai da […]
Tsohon dan tawayen kasar Congo, Mista Bosco Ntaganda, ya gurfana a gaban Kotun Duniya (ICC) mai hukunta laifuffukan yaki, inda ya ce ba ya da laifi a kan tuhumar da kotun ke masa ta laifufukan yaki.
Kotun, wacce ke birnin Hague, tana tuhumar Ntaganda ne da aikata laifuffukan yaki 18, cikinsu har da kisan kai da yi wa yara fyade da tursasa wa mata yin lalata.
Kotun ta ce Ntaganda ya aikata wadannan laifuka ne a gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo a tsakanin shekarar 2002 zuwa 2003.
Mista Ntaganda, wanda dama an sa ran zai ki amsa laifuffukansa, ya yi tozali da dimbin mutanen da suke zargin ya ci zarafinsu.
A shekarar 2013 ya mika kansa, inda ya bukatar a mika shi ga kotun ta ICC, bayan ya kwashe shekara da shekaru a fagen daga.
Ana yi masa lakabi da Terminator, saboda shaharar da ya yi wajen kisan kai na ba-sani-ba-sabo.
Mista Ntaganda na daga cikin wadanda kotun ICC ke nema ruwa a jallo.