NUC ta umarci jami’o’i su fara shirin budewa

Hukumar Kula da Jami’o’i ta umarce su da su fara shirye-shirye nan take

NUC ta umarci jami’o’i su fara shirin budewa

Hukumar Kula da Jami’o’i ta Najeriya (NUC) ta umarci dukkannin jami’o’i da su fara shirye-shirye nan take domin ci gaba da karatu baya rufe sakamakon bullar cutar COVID-19.

Sanarwar da NUC ta aike wa Shugabannin Jami’o’i ta ce hakan na zuwa ne duba da raguwar masu cutar da bullarta ta sa aka rufe makarantun a a ranar 23 ga watan Maris, 2020.

“Sakamakon jawabin Kwamitin Shugaban Kasa kan Yaki da COVID-19 cewa an samu raguwar masu cutar sosai, Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta amince da bukatar NUC na cewa jami’o’i su fara shirye-shirye nan take domin ci gaba da harkokin karatu”, inji sanarar.

Ka’idojin bude jami’o’i

Sai dai hukumar ta gindaya sharudda biyar da ya wajaba kowace jami’a ta cika kafin a bude ta domin gaba da karatu.

  1. Dole a kiyaye matakan kariyar da tsare-tsaren Hukumar Yaki da Cutttuka Masu Yaduwa ta Kasa (NCDC) na hana yaduwar cutar.
  2. Babu dalilin da zai sa a rusa tsarin zangon karatun NUC da ya danganci adadin kwanakin kowane zangon karatu.
  3. Dole ne a tabbatar da kiyaye dukkannin dokoki da ka’idojin NUC na tabbatar da inganci.
  4. NUC da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya za su kai ziyarar gani da ido domin tantance irin tsare-tsaren kare lafiya da ingancinsu a jami’o’i ta bangaren kayan aiki, dakunan karatu, ofisoshi, ajujuwa, dakunan kwanan dalibai, dakunan gwaje-gwaje, cibiyoyin kula da lafiya da sauransu.
  5. Dole ne daga lokaci zuwa lokaci jami’o’in za su rika sanar da NUC game da halin da suke ciki.