Nuhu Ribadu: Alakakai kadagaren bakin tulu

Abin da ya ba ka tsoro wata rana zai ba ka tausayi, domin a rayuwa babu wani abu mai tabbata sai abin da Jalla Ya hukunta. Kowa dai a kasar nan, hatta na goye, ya san Malam Nuhu Ribadu da kuma irin gwagwarmayar da ya yi don maganin azzaluman da suka handame dukiyar talakawa, suka […]

Nuhu Ribadu: Alakakai kadagaren bakin tulu
Nuhu Ribadu: Alakakai kadagaren bakin tulu

Abin da ya ba ka tsoro wata rana zai ba ka tausayi, domin a rayuwa babu wani abu mai tabbata sai abin da Jalla Ya hukunta. Kowa dai a kasar nan, hatta na goye, ya san Malam Nuhu Ribadu da kuma irin gwagwarmayar da ya yi don maganin azzaluman da suka handame dukiyar talakawa, suka bar su a kwankwance, suna ta kukan banza. A zamanin da yake shugaban hukumar yaki yi wa tattalin arziki ta’annati, ya ga abin tsoro game da facakar da aka yi da dukiyar kasar nan, ya kuma zame abin tsoro, domin ya bi ya danke wadanda suka hadidiyi dukiyar bayin Allah, ya kuma tursasa su sai da suka haras, aka kuma wurga su a gidan kaso, inda suka yi asarar mutuncinsu.
Nuhu ya yi aikinsa, an kuma yaba masa, mazambata sun shiga taitayinsu. Kamar yadda ya yi ta  farautar mahandama haka ne ma masu babakere kan dukiyar jama’a ke yakarsa, kuma sai da suka ga bayansa. Ashe dai da gaske ne da ake cewa abin kirki bai karbi kare ba, ko ya yi ma dukansa ake yi, sai ga shi nan an yi wa Malam Nuhu korar karen. Jama’a ba su ji dadin ganin yadda Malam Nuhu ya yi karkon kifi ba a aikin yaki da rashawa, an  kuma jajanta masa  don an ci zalunsa, an kuma tozarta shi, aka nuna masa iyakarsa, saboda ya tsaya kan gaskiya, ya kuma kyamaci ha’inci da maciya amanar talakawa.
Wannan ne ya sa Malam Nuhu ya shiga dandalin siyasar kasar nan da kafar dama, inda duk ya karkata akalarsa sai jama’a su yi dafifi, domin yi masa kyakkyawar marhaban, a ko ina kuma ya zama dan lelen da ake tarairaya kamar zinariya. Kai hatta a shiyyar da al’ummomin cikinta ba su ra’ayin Hausa-Fulani sai da suka rungume shi hannu bibbiyu, suka fifita shi kan jinsinsu, suka daga shi kololuwa, suka sanya shi a gaba don ya yako masu kujerar shugabancin kasar nan.
Bayan hakan ba ta yiwu ba, Malam Nuhu bai karaya ba, ya ci gaba da gwa-gwa-gwa tare da ‘yan gwagwarmayar da suka dage don ganin bayan zaluncin da shugabanni da mabiya jam’iyyar PDP ke yi wa talakawan kasar nan, sa’ilin da ya rankaya tare da ayarin jam’iyyar APC da talakawa suka sanya a gaba. Malam Nuhu na daga cikin wadanda jam’iyyar ke ji da su, kuma ma har wasu sun fara yi masa lakabin Halifan Buhari, domin sun san shi ne kadai zai iya kwatanta tsabar gaskiya da rikon amana, da gudun abin duniya da tausayin talakawa da tsananin kishin kasa kaman  Buhari, Gwarzon talakawa.
Amma kash! Tun tafiyar ba ta kai ko ina ba sai ga Malam Nuhu ya sare, bayan wasu sun shafa masa mai a baki don ya koma jam’iyyar PDP, inda aka yi masa tayin mukamin Gwamnan Jihar Adamawa.
Jama’ar da suka fara jin wannan labarin nan take suka karyata, domin sun san Malam Nuhu mutum ne mai akida ne, wanda da wuya ko wani rashi ba su sa shi kauce hanya. Amma ina! Malam Nuhu ya saki reshe, ya kama ganye, kuma sai bayan ya subuto ne zai gane cewa ashe dai  ba shi da wayo, domin zai kasance ba shi ga addini, ba shi kuma ga adila.
A’aha, don me za a ce Nuhu zai yi batan bakatantan, zai rasa tsuntsu, ya kuma rasa tarko, alhali masu abin ne suka daure masa gindi bayan sun karya laggonsa? Ai idan ka ji a gudu da labari, kuma makaho ba zai ce a yi wasan jifa ba sai idan ya taka dutse. E, to, idan haka ne Malam Nuhu na da hujjar canja sheka daga APC zuwa PDP don ya zama gwamna, tun da ba abin kunya ne ba ga ‘yan siyasar Najeriya su ci baya a hankoronsu na neman mukami.  Ba ga shi nan ba gwamnoni na takarar kujerar dan majalisar dattijai  bayan saukarsu? Kaico! Dangane da haka ba mamaki idan Malam Nuhu ya gwammace takarar gwamnan Jiha daga ta Shugaban kasa da ya taba yi, kuma idan ya sha kasa watakila ya sake jarraba takarar shugaban karamar hukuma. Kinjalaye, girma ya fadi Alasure.
To amma me za a kira wannan al’amari na Malam Nuhu: batar basira ce haka da rana tsaka, ko kuwa rashin mafadi ne ya kai shi amincewa a cije shi sau biyu a rami guda?  To ai an ce kura ta san gidan mai babban  sanda. Malam Nuhu dai ya san abin da ya baro a PDP, kuma shi da kansa ne ya yanke shawarar komawa. Amma kuwa zai sha mamaki! Ai ba mahaukacin kare ne ya ciji shugabannin jam’iyyar PDP ba  da har za su bari Nuhu ya ci zabe, daga bisani kuma ya haramta musu dukiyar talakawa. An ce amfanin zunubi romo, kuma saboda su sassaci dukiyar talakawa  ne suke son tsayar da wanda zai taimaka musu satar dukiyar talakawa. Idan har Nuhu ya ci zabe su ba za su ci ba. Malam Nuhu dai ba zai daga wa mahandama kafa su tatike Jihar Adamawa ba, to ina ranarsa a gare su? Idan bai ci ba zai gamu da jidali, idan ya ci zai zame alakakai kadangaren bakin tulu, to ina  amfanin badi ba rai?