NURTW ta kasa ta bude ofishin shiyya a Zamfara
kungiyar Direbobi ta NURTW karkashin jagorancin shugabanta na kasa Alhaji Najim Yasin ta bude sabon ofishin shiyya na shida a Jihar Zamfara a ranar Talata. Alhaji Najim ya ce kungiyar ta gina sabon ofishin ne a Zamfara don samar wa mambobinta sauki wajen gudanar da harkokin kungiyar.Ya ce kungiyarsu tana da ofishi a Kano da […]
kungiyar Direbobi ta NURTW karkashin jagorancin shugabanta na kasa Alhaji Najim Yasin ta bude sabon ofishin shiyya na shida a Jihar Zamfara a ranar Talata.
Alhaji Najim ya ce kungiyar ta gina sabon ofishin ne a Zamfara don samar wa mambobinta sauki wajen gudanar da harkokin kungiyar.
Ya ce kungiyarsu tana da ofishi a Kano da Kaduna amma haya suke yi, “wannan ya sa mu ka ga dacewar mu gina ofishinmu na dindindin, inda muka yanke shawara a gina shi a Zamfara, saboda samar wa ’yan kungiya sauki wajen gudanar harkokin kungiyar shiyyarmu. Babban burina in gina irin wannan ofishi a kowace shiyya a Najeriya.”
“Mun mallaki wannan filin da muka gina ofishin ne tun lokacin mulkin soja, wato lokacin Jibrin Bala Yakubu, wanda kuma cikin ikon Allah Ya a lokacina ne aka gina wannan ofishi.
“Aikin wannan ofishi na shiyya ta shida zai hada da Jihar Kaduna da Kebbi da Zamfara da Katsina da Jigawa da kuma Sakkwato, duk wadannan jihohi za su samu sauki idan suka gudanar da taro a Zamfara, kowa zai koma jiharsa cikin sauki ba tare da wata matsala ba.” Inji shi.
Shugaban kungiyar na shiyya na shida Alhaji Kiruwa ya bayyana farin cikinsu da samun wannan ofishi na miliyoyin Naira.
Ya ce: “Kuma wannan ya sa a yanzu muka dauki alkawarin ba shugaban kungiyar na kasa dukkan hadin kai don neman karin wa’adin shugabancin kungiyar. Nan gaba wannan ofishi a Jihar Zamfara zai zama abin alfahari ga kowane dan kungiya.
Ya bukaci membobin kungiyar shiyya ta shida su kara hada kansu, sannan taimaka wa shugabansu Alhaji Najim Yasin ya cika alkawuran da ya dauka na gina ofisoshi a sauran shiyyoyin kasar nan, sannan su ci gaba da addu’a don kungiyarsu ta rika samun nasara a dukkan kudirinta.