NURTW ta shawarci mambobinta kan inshora

kungiyar direbobi ta NURTW ta bayyana aniyarta na cigaba da taimakawa mambobinta a kowane lokaci bukatar hakan ya taso. Shugaban kungiyar reshen jihar Neja, Alhaji Garba Musa Bala ne ya bayyana hakan a lokacin da kungiyar ta karbi bakuncin masu zuwa gaisuwa, sanadiyar rasa sakataren kungiyar ta jihar Neja, Kwamared Nasiru Aliyu da ta yi […]

NURTW ta shawarci mambobinta kan inshora

kungiyar direbobi ta NURTW ta bayyana aniyarta na cigaba da taimakawa mambobinta a kowane lokaci bukatar hakan ya taso. Shugaban kungiyar reshen jihar Neja, Alhaji Garba Musa Bala ne ya bayyana hakan a lokacin da kungiyar ta karbi bakuncin masu zuwa gaisuwa, sanadiyar rasa sakataren kungiyar ta jihar Neja, Kwamared Nasiru Aliyu da ta yi ranar littinin din makon nan.

Alhaji Garba ya ce Inshora abu ne mai amfani ga direba, domin a duk lokacin da wani tsautsayi ya taso yakan samu hanyar samun tallafi cikin sauki, jama’armu ba su dauki tsarin inshorar rai da lafiya da muhimmanci ba saboda ita kungiyar, kungiya ce mai zaman kanta ba ta tilasta duk wani da bai cikin dokokinta, amma dai yana da kyau duk ita kanta kungiyar idan wani al’amari ya samu direba na rasa lafiya ne ko rai akwai irin tallafin da ta ke bayarwa na tausayi gare shi ko iyalansa.

Yanzu kungiyarmu ta NURTW ta himmantu wajen tallafawa direbobi ta hanyar ba su tallafi na aiki ko kuma na kai dauki ga wani abu da ya same su, idan direba ya rasa ransa kungiyar kan dauko wani daga cikin iyalinsa dan maye gurbinsa da aiki, haka idan ya bar yara kananan mukan dauki nauyin karatunsu da kuma taimakawa ga iyalan mutum na abinci da wasu abubuwan da ba su fi karfin kungiyar ba.

Kwamared Nasiru Aliyu dai ya rasu ya bar matan aure biyu da yara shida. Da yake karin haske akan lamarin kungiyar, tsohon shugaban kungiyar, Alhaji Abubakar Musa Suleja, ya ce lallai NURTW na daya daga cikin kungiyoyin da ke kula da mambobinsu akan haka ne Allah ke sanya albarka ga cigaban ita kungiyar. Ya kara da cewar lallai dambu idan ya yi yawa ba ya jin mai, NURTW za ta cigaba da kokarinta na ganin tana kokarin bada tallafi ga mambobinta.