Nusrat Chowdhury: Musulma ta farko da ta zama Alkalin Tarayya a tarihin Amurka

Lauyar kare hakkin jama’a da ta yi fice.

Nusrat Chowdhury: Musulma ta farko da ta zama Alkalin Tarayya a tarihin Amurka

Majalisar Dattawa ta tabbatar da Nusrat Chowdhury, wata lauya mai kare hakkin jama’a, a matsayin Musulma ta farko da ta zama Alkalin Tarayya a tarihin Amurka.

Za ta kasance a wannan matsayi na tsawon rayuwarta a Kotun Tarayya ta Brooklyn da ke New York bayan kada kuri’a 50-49 ranar Alhamis bisa ga jam’iyya.

Tabbatar da mukamin na ta ya janyo yabo daga Kungiyar ’Yancin Jama’a ta Amurka, inda ita ce Daraktan Shari’a na ACLU na Illinois.

Kafin wannan matsayi, ta yi aiki daga 2008 zuwa 2020 a ofishin ACLU na kasa, ciki har da shekaru bakwai a matsayin Mataimakiyar Daraktan Shirin Tabbatar Da Adalcin Launin Fata na ACLU.

A cikin wani sakon Twitter, ACLU ta kira ta “lauyar kare hakkin jama’a da ta yi fice.”

Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa, Chuck Schumer, D-N.Y, wanda ya nemi a zabe ta, ya ce ta kafa tarihi a matsayin Ba’amurka ‘yar asalin Bangladesh ta farko kuma Musulma ta farko da ta zama alkali ta tarayya.

Bayan kammala makarantar shari’a, Chowdhury ta yi aiki a birnin New York a matsayin alkalin gundumar Amurka.

Ta kuma yi aiki a Kwamitin Aiki Da Cikawa Na Shugaban Kasa kan Tabbatar Da Amincewar Jama’a a Tsarin Adalci na Amurka.

Nadin nata ya yi daidai da alkawarin da Shugaba Joe Biden ya yi na jaddada tsarin tafiya da kowane jinsi ko launi a nade-naden fannin shari’a.

AP

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja