Nutsewar jirgin Koriya ya sa Firaministan kasar yin murabu
Firaministan Koriya ta Kudu Chung Hong-won ya yi murabus biyo bayan zargin sakaci da ake wa gwamnatinsa a nutsewar wani jirgin ruwan kasar wanda ya nutse a ranar 16 ga watannan.Ya ce ya dauki wannan matakin ne saboda a cewarsa halin da iyalan fasinjojin ke ciki na hana shi barci a kowane dare. Sai dai […]

Firaministan Koriya ta Kudu Chung Hong-won ya yi murabus biyo bayan zargin sakaci da ake wa gwamnatinsa a nutsewar wani jirgin ruwan kasar wanda ya nutse a ranar 16 ga watannan.
Ya ce ya dauki wannan matakin ne saboda a cewarsa halin da iyalan fasinjojin ke ciki na hana shi barci a kowane dare. Sai dai firaministan zai ci gaba da kasancewa a kujerarsa har sai an kammala aikin binciken nutsewar jirgin.
Jirgin mai suna Sewol da ke dauke da fasinjoji 476 wanda yawancinsu dalibai ne, ya nutse ne a gabar tekun Koriya ta Kudu inda hukumomi suka tabbatar da mutuwar mutane 187. Sai dai kuma har yanzu ba a san inda sauran fasinjojin suke ba amma ana kyautata zaton cewa ruwa ya ci su.
Iyalan fasinjojin dai sun dora alhakin mutuwar ‘yan uwansu da yadda hukumomi kasar suka gudanar da aikin ceton da tafiyar hawainiya.
A wani jawabi ta tashar talabijin din kasar, Firaministan ya ce: “Wannan lokaci ne da ya dace a ce na dauki alhakin abin da ya faru, kuma zan yi hakan ne kawai ta hanyar sauka daga kujerata.” Inji shi.
Ya kara da cewa: “A madadin gwamnatinmu ina mai neman gafara dangane da rashin daukar matakan da za su kiyaye faru wannan hadarin da kuma abin da ya shafi daukar matakan gaggawa bayan faruwarsa. Kuma ina fatan cewa wannan ne hadari na karshe da kasarmu za ta fuskanta.” Inji shi.