Nyako da Gaidam da wasu sun soki neman kara wa’adin dokar ta-baci

Gwamnan Jihar Adamawa Murtala Nyako da takwaransa na Jihar Yobe Ibrahim Gaidam sun nuna adawa kan bukatar Shugaban kasa Goodluck Jonathan ta neman a kara wa’adin dokar ta-baci a jihohi uku na Arewa maso Gabas.Shugaba Jonathan ya mika wa Majalisar Dattawa bukatar kara wa’adin dokar ta-bacin, wadda ta fara aiki sheakara daya da ta gabata […]

Nyako da Gaidam da wasu sun soki neman kara wa’adin dokar ta-baci
Nyako da Gaidam da wasu sun soki neman kara wa’adin dokar ta-baci

Gwmnan Jihar Yobe Alhaji Ibrahim GaidamGwamnan Jihar Adamawa Murtala Nyako da takwaransa na Jihar Yobe Ibrahim Gaidam sun nuna adawa kan bukatar Shugaban kasa Goodluck Jonathan ta neman a kara wa’adin dokar ta-baci a jihohi uku na Arewa maso Gabas.
Shugaba Jonathan ya mika wa Majalisar Dattawa bukatar kara wa’adin dokar ta-bacin, wadda ta fara aiki sheakara daya da ta gabata a jihohin Borno da Adamawa da Yobe zuwa wasu watanni shida.
A wata takardar da ya aike wa Majalisar Dattawan da shugaban majalisar, Sanata Dabid Mark ya karanta a zauren majalisar, Shugaba Jonathan ya ce ya bukaci a tsawaita dokar ta-bacin ne domin a tabbatar da tsaro a jihohin.
Dokar dai za ta kare aiki ne a ranar Litinin mai zuwa.
A martanin Gwamna Nyako ta hannun kakakinsa Ahmed Sajo ya ce Adamawa ta fi Abuja zaman lafiya, inda ya bukaci majalisar dokoki ta kasa da ta tura kwamitin bin diddigi zuwa Adamawa don duba halin da tsaro yake ciki a jihar, domin su yanke shawara kan matakin da za su dauka kan dokar ta-bacin.
Ya ce, “A karkashin dokar ta-bacin ne aka sace dalibai fiye da 200, kuma aka yi tafiyar sama dab kilomita 100 da su, ba tare da wani ya tare su ba. Ka ji mamakin yadda jami’an tsaro za su musguna maka idan da kaji 200 za ka dauko a jihohin uku. Don haka an ba mu kunya da wasu mutane da suike zaune a Abuja suka yanke shawarar a tsawaita dokar ta-bacin.”
Daga Damaturu, Kakakin Gwamnan Jihar Yobe Abdullahi Bego ya ce, dokar ba ita ce mafita ga matsalar tsaro da ke addabar jihohin uku ba, idan aka lura da yadda ta gaza cimma manufar kafa ta wata 12 da suka gabata.
Shi kuwa Gwamnan Jihar Borno, ta bakin kakakinsa Isa Umar Gusau, ya ce abin da ya fi damunsa a yanzu shi ne batun ceto ’yan matan Chibok, kuma yana nazartar bukatar karin wa’adin.
Sai dai kakakin kungiyar Dattawan Jihar Borno, Dokta Bulama Mala Gubio ya soki shirin kara wa’adin dokar. “Lallai sojoji sun yi kokarinsu a bara, amma nasarar da suka samu ta samu ne bisa goyon bayan da suka samu daga gwamnatin dimokuradiyya da ke jihar da hadin kan ’yan banga. A fahimtarmu sojoji za su iya yin duk aikin da aka dora musu ba tare da dokar ta-baci ba,” inji shi.
Wasu sanatoci da ’yan majalisar wakilai da suka fito daga jihohin da dokar ke aiki sun nuna adawa da kara wa’adinta.