Nyako ya gamu da sharrin siyasa
Batun tsige Murtala Nyako daga mukamin Gwamnan Jihar Adamawa abin takaici ne, amma sai dai bai ba kowa mamaki ba, domin kuwa kowa ya san za a rina, wai an saci zanin mahaukaciya. Ba wani abu ne makasudin kawar da Nyako illa ce biye da son zuciya, domin kuwa laifuffukan da aka zarga a wuyansa, […]
Batun tsige Murtala Nyako daga mukamin Gwamnan Jihar Adamawa abin takaici ne, amma sai dai bai ba kowa mamaki ba, domin kuwa kowa ya san za a rina, wai an saci zanin mahaukaciya. Ba wani abu ne makasudin kawar da Nyako illa ce biye da son zuciya, domin kuwa laifuffukan da aka zarga a wuyansa, shi da mataimakinsa ba, ba sababbin al’amura ne ba a harkokin gudanar da mulki, kuma ba kansa ne farau ba, amma wadanda suka riga shi aikata haka alhali suna kan kujerun mulki babu abin da ya same su, duk kuwa da cewa an sha samunsu dumu-dumu da aikata almundahanar da ta ninka tasu ninkin-bainininki. Shi ya sa ake cewa barawon da ba a gani ba susansa Mahamman.
Tun daga lokacin da aka fara makircin kai Nyako kasa ya rigaya ya san cewa siyasa ce ta haddasa haka, ba wai kishin al’ummar Jihar Adamawa ne ba, sai dai dukiyarsu da ake cewa wai ya hadiya. Ya sha nuna yatsan zargi ga wadanda ya kira ‘yan siyasar Jihar Adamawa mazauna Abuja, kuma makiya jama’a, wadanda bakin burinsu ne ya haddasa haka. Wadannan mutanen da yake kuka da su game da neman ganin bayansa duk ‘yan jam’iyyar PDP ne, kuma wasunsu batun addini ya makanta su, ya kuma bakanta zukatansu; wasu kuma burinsu shi ne maye gurbinsa da wanda ya fito daga tsatsonsu, don su ji dadin juya gwamnatin da za ta kafu a bayansa, su ma su yi ta tumurmusar dukiyar jama’a ba mai kwabarsu. To ko ma dai mene ne gaskiyar wannan kazafin, ta Nyako ta kare, saura kuma ta magabtansa.
Hakan nan kuma ta daya bangaren ana iya cewa da hannun jam’iyyar PDP, wacce a da can ta dauki Murtala Nyako tamkar dan lelenta, shi kuma ya fi kowa zakewa wajen nuna goyon baya da kare sukar da ake yi wa Shugaba Goodluck Jonathan. To amma kwance wa jam’iyyar zani da ya yi a kasuwa, sakamakon dambarwarsa da ‘yan siyasar Jihar Adamawa mazauna Abuja, sai ga Nyako ya yi kaura zuwa jam’iyyar adawa ta APC, ya kuma nemi ya karya wa Shugaba Jonathan tsinken tsire a ido yayin da yi zargin cewa shi ne ummul-haba’isin yamutsin da ke wanzuwa a Arewacin kasar nan. Ya kuwa furta haka ne yayin da ya bayar da wata lacca a kasar Amurka, wacce Jonathan da makararrabansa ba su ji dadin tonon sililin da ya yi masa ba a kasar iyayen gidansa. Yanzu sai a jira a ga irin kullin da gwamnatin PDP za ta bi Nyako da shi, tun da ta kayar da shi kasa warwas. Za ta hau ruwan cikinsa ne, ta yi ta tittika, ko danke shi za ta yi, ta gurfanar da shi gaban kotun da za ta mayar da shi fursuna don alkadarinsa a siyasance ya karye, ko kuwa uzzura masa za a yi har sai ya tsallake, ya bar kasar don kada sabuwar jam’iyyar da ya koma ta yi tasiri a 2015?
Wannan shi ne tushen azazzala wa Nyako, domin kuwa jam’iyyar PDP ta fahimci irin raunin da take da shi a wasu jihohi da ma kasar baki daya, shi ya sa ta bazama, tamkar bakar kurar da yunwa ta haukata, don kwace jihohin jam’iyyar adawa da karfi, da jayi, kuma ko sama da kasa za ta hade ba ta damu ba. A yanzu ai ga shi nan ta hura wa Gwamnan Jihar Nasarawa, Umar Tanko Al-makura wuta, kuma idan ba wani ikon Allah ba sunansa tsigagge. To wai shin gwamnonin shiyyoyin Kudu-maso-gabas da ta Kudu-Kudu ma’asumai ne, ba su aikata laifin komai, domin su ‘ya’yan jam’iyyar PDP ne, ko kuma suna daga cikin wadanda ke amfani da addini da kabilanci domin samun gindin zama, ba su duntsar dukiyar talakawa ne, su yi ta tsuku? Me ya sa su ba a yi masu tonon silili balle har ta kai ga karya masu irli? Su shafaffu da mai ne illa Gwamna Rotimi Amechi, wanda ya fandare, ya kulla abokanta da wadanda suke kyama. Wannan babbar magana ce mai cike da hatsarin gaske game da hadin kan kasar nan da kuma dorewar dimokuradiyyar da ake kwarzantawa.
A yanzu dai Gwamna Nyako ne gwamna na biyar da aka yi wa yankan kauna, aka tsige shi saboda siyasa tun daga mayar da mulki ga farar hula a shekarar 1999, Gwamnan Jihar Anambra Chris Ngige ne aka fara kawarwa ta wannan hanyar, sai kuma Dieprieye Alamieseigha na Jihar Bayelsa da aka tumbuke a watan Disambar 2005, baicin shi kuma sai Gwamnan Jihar Filato, Joshua Dariye, da aka kafa wa dokar ta baci a jiharsa a watan Nuwambar shekarar 2006, aka jingine shi na tsawon watanni shida. Kafin nan sai da aka tuntsurar da Gwamna Ayodele Fayoshe na Jihar Ondo a watan Oktobar shekarar 2006. Dukkansu sun kau ne saboda rikice-rikicen siyasar da ta kaure tsakaninsu da gwamnatin tarayya, aka kuma nuna masu iyakarsu.
Idan dai rashawa ko ha’inci da rashin aminci ne suka sa aka tozarta su haka, ai da yanzu babu sauran wani jami’in gwamnati ko wanda ke rike da mukamin siyasa da yake ci gaba da aikata wannan mummunar dabi’ar, domin kuwa ganin yadda aka yi da su zai sa wasu tsoron Allah. Lallai siyasa mugun wasa ne, komai iyawarka sai an ji maka.