NYSC: Babu ranar bude sansanoni
Hakumar da ke kula da matasa masu yi wa kasa hidima ta Najeriya (NYSC) ta ce ba za ta bude sansanoninta ba har sai yanayin annobar COVID-19 ya yi sauki a kasar. Hukumar ta sanar da hakan cikin wata takarda da ke karyata jita-jitar cewa za ta bude sansanoninta a fadin Najeriya. Takardar da Darektan […]
Hakumar da ke kula da matasa masu yi wa kasa hidima ta Najeriya (NYSC) ta ce ba za ta bude sansanoninta ba har sai yanayin annobar COVID-19 ya yi sauki a kasar.
Hukumar ta sanar da hakan cikin wata takarda da ke karyata jita-jitar cewa za ta bude sansanoninta a fadin Najeriya.
Takardar da Darektan Hulda da Jama’an NYSC, Adenike Adeyemi, ya fitar, ta jaddada muhimmancin lafiyar matasan da ma’aikatanta da sauran mutanen da ke alaka da sansanonin ga ga hukumar.
- An nada dan NYSC sabon Hakimin Yantumaki
- Za a fara daukar sabbin ‘yan N-Power —Minista
- Gaskiya ne ba mu biya ‘yan N-Power 12,000 hakkokinsu ba —Gwamnati
“Wannan na daga cikin dalilanmu na rufe rukunin (Batch A) na matasa masu yi wa kasa hidima a watan Maris, 2020. Ba za mu taba yin abin da zai kawo barazana ga lafiyarsu ba.”
Hukumar ta ce ko da ta tabbatar cewa annobar ta lafa, ba za ta bude sansanonin ba har sai Gwamnatin Tarayya ta umarce ta da yin hakan.
Ta kuma yi kira ga matasan da wadanda suke bisa layin fara shirin da su yi watsi da duk wani labari da za su ji kan sansanonin matukar ba daga NYSC suka ji shi ba.
Adeyemi ta ce Shugaban, Shuaibu Ibrahim, na kiran matasan da su ci gaba da kiyaye ka’idojin kariya daga kamuwa da annobar, kamar yin amfani da kyallen rufe fuska da wanke hannu da dai sauransu.