NYSC ta kama masu yi wa kasa hidima 10 da takardun bogi

Hukumar Kula da Masu Yi wa Kasa Hidima (NYSC) ta yi nasara kama wasu  mutum 10 da suka yi yunkurin yin rijista da hukumar da takardun bogi a sansanonin Hukumar da ke jahohin Najeriya. Daraktan watsa labarai kuma jam’in hulda da jama’a na NYSC Adenike Adeyemi, ne ya sanar da hakan. Uku daga cikin masu […]

NYSC ta kama masu yi wa kasa hidima 10 da takardun bogi

Hukumar Kula da Masu Yi wa Kasa Hidima (NYSC) ta yi nasara kama wasu  mutum 10 da suka yi yunkurin yin rijista da hukumar da takardun bogi a sansanonin Hukumar da ke jahohin Najeriya.

Daraktan watsa labarai kuma jam’in hulda da jama’a na NYSC Adenike Adeyemi, ne ya sanar da hakan. Uku daga cikin masu laifin an kama su ne a sansanin jihar Taraba. Inda suka ce sun kammala jami’ar Istop da ke Cotonou a jamhoriyar Benin. Mutum ukun su ne Nasiru Yau, Shehu Muktar da  Iliyasu Usman.

An kuma kama wasu ‘yan mata biyu da takardun bogin a sansanin su da ke Katsina.

Daga cikin su mai suna Offor Chinelo Blessing, daga Jami’ar Jihar Imo da jabun digiri a bangaren Inshora. Sai  Kuma wadda ake zargi mai suna Meaienwa Chimdinma Ngozi, an kamata da digirin kan Turanci na jabu na jamiar Jihar Imo.

Sai kuma an sansanin NYSC na jihar Kebbi an kama mutum 4 da suka hada da: Nwachukwu Chimaobi Curtis, Ononuju Amarachi Nwamaka, Francis Joseph Arinze da Chigozie Evidence Chijioke, duk da takardun digirin bogi daga jami’ar jihar Imo.