NYSC ta sanar da ɓacewar shugabanta na Akwa Ibom

an sace su ne a cikin wata ƙirar Hilux fara mai lamba “27D31FG”.

NYSC ta sanar da ɓacewar shugabanta na Akwa Ibom

Hukumar Yi Wa Ƙasa Hidima (NYSC) ta sanar da cewa shugabanta na Jihar Akwa Ibom, Mista Okun Christopher da direbansa, Mista Daniel Effiong Asibong, sun ɓace.

Da yake zantawa da manema labarai a Abuja, Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Hukumar, Eddy Megwa ya ce an sace su ne a tsakanin jihohin Delta da Akwa Ibom a lokacin da suke tafiya aiki a ranar Litinin, 29 ga Yuli, 2024.

Megwa ya koka da cewa tun daga lokacin da aka sace su, duk ƙoƙarin gano inda suke bai cimma ruwa ba.

Ya ce hukumar na ci gaba da tuntuɓar iyalansu da makusanta a yunƙurinta na samun duk wasu bayani da za su taimaka domin gano inda suke.

Megwa ta roƙi duk wanda ke da sahihan bayanai da za su taimaka wajen gano wadanda abin ya shafa da su miƙa bayanan ga reshen hukumar mafi kusa.

Ya ce “motar da suke tafiya da ita ƙirar Hilux ce fara mai lamba “27D31FG”.

“Duk wanda yake da cikakken bayani game da inda suke to ya tuntuɓi sakatarorin NYSC na jihohi 36 ko ofisoshin yanki ko hedkwatar daraktoci ta ƙasa da ke Abuja ko ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko wasu hukumomin tsaro domin ɗaukar matakin gaggawa,” inji shi.

DSS ta kama ’yan Boko Haram 10 a Osun

Mutum 60 sun mutu a fashewar tankar mai a Neja

Solskjaer ya zama sabon kocin Besiktas

Nijeriya ta zama abokiyar hulɗar ƙungiyar BRICS