NYSC ta tura wa mai yi wa kasa hidima dubu 330 bisa kuskure

Matashiyar ta ce a shirye take ta mayar da kudin ga gwamnati

NYSC ta tura wa mai yi wa kasa hidima dubu 330 bisa kuskure

Wata matashiya mai yi wa kasa hidima ta ce hukumar NYSC ta tura mata Naira dubu 330,000, a maimakon N33,000 alawus dinta, bisa kuskure.

Gwamnatin Najeriya dai na biyan matasan da ke yi wa kasa hidima N33,000 a kowanne wata.

To sai dai a wani bidiyo da ta watsa a kafafen sada zumunta na zamani, matashiyar ta yi ikirarin cewa NYSC ta tura mata kusan ninki 10 na abin da ya kamata a biya ta a wata.

A cikin bidiyon dai, matar, wacce ke sanye da farar riga da hular NYSC, tana neman shawarar masu amfani da shafukan kan me ya kamata ta yi da kudin.

Daga nan ne sai ta nemi shawarar matakan da ya kamata ta bi domin ta mayar da kudin ga gwamnati. (The Nation)

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan

Tags