NYSC: Za a bude sansanoni ranar 10 ga Nuwamba

Ministan Wasanni ya ce za a bude sansanonin NYSC cikin tsauraran matakan kariyan COVID-19

NYSC: Za a bude sansanoni ranar 10 ga Nuwamba

Ministan Wasanni da Harkokin Matasa, Sunday Dare ya sanar da bude sansanonin masu yi wa kasa hidima (NYSC) a fadin Najeriya daga ranar 10 ga watan Nuwamba.

A sakon da ya fitar a safiyar Alhamis, Ministan ya ce za a bude sansanonin NYSC din ne cikin tsauraran matakan kariyar COVID-19.

Bude sansanonin na zuwa ne wata bakwai bayan rufe su sakamakon bullar annobar COVID-19, wadda da tilasta sanya dokar kulle da hana taruwan jama’a.

A watan Maris ne hukumar ta umarci matasa da ke rukunin farko a kashin farko na 2020 da su fara zuwa wuraren aikin da ta tura su.

A lokacin ta ce “za a gayyace su da su koma sansanin horaswa idan al’amura suka daidaita kamar yadda aka yi a shekarun baya da aka samu bullar cutar Ebola”.

Mahaifinmu ba shi da ciwon suga – Ɗan Janar Rabe

Sojoji sun daƙile harin Boko Haram, sun ceto mutum 9 a Borno

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo