Obama ga Jonathan: Ka guji saurin yanke hukunci
Shugaban Amurka Mista Barrack Obama da Babbana Sakataren Majalisar dinkin Duniya Mista Ban Ki-moon sun yi Allah wadai da harin bam da aka kai a garin Nyanya da ke wajen Abuja inda fiye da mutum 70 suka mutu a ranar Litinin da suka gabata.Sai dai Shugaba Obama ya shawarci Shugaba Goodluck Jonathan ya guji saurin […]

Shugaban Amurka Mista Barrack Obama da Babbana Sakataren Majalisar dinkin Duniya Mista Ban Ki-moon sun yi Allah wadai da harin bam da aka kai a garin Nyanya da ke wajen Abuja inda fiye da mutum 70 suka mutu a ranar Litinin da suka gabata.
Sai dai Shugaba Obama ya shawarci Shugaba Goodluck Jonathan ya guji saurin yanke hukunci kan hare-haren da ake kaiwa a Najeriya tare da kiran gwamnatin ta gudanar da cikakken bincike kan harin.
Wata sanarwa daga kakakin sashin harkokin wajen Amurka, Jen Psaki a ranar Talata ta ce Shugaba Obama ya yi Allah wadai da harin, inda ya ce gwamnatinsa ta kadu da wannan ta’addancin rashin imani da ake yi ga fararen hulan da ba su san hawa ba ba su san sauka ba a Najeriya. Obama ya kuma yi Allah wadai da hare-haren da aka kai kauyuka uku na Jihar Borno inda aka halaka kusan mutum 100 a karshen mako, ya karfafa gwamnati ta gudanar da cikakken bincike domin bankado masu kai hare-haren tare da hukunta su.
“Za mu ci gaba da kasancewa tare da gwamnati da al’ummar Najeriya a yayin da suke fama da mugun ta’addanci. Shugaban Najeriya ya zargi Boko Haram da kai harin Abuja, mun ga haka, amma a saninmu babu wata kungiya da ta yi da’awar daukar nauyin harin tukunna. … A fahimtarmu riga malam masallaci ne a yanke wancan hukunci (na jingina harin ga Boko Haram),” inji Obama a cikin sanarwar.
Shi kuwa Ban Ki-moon kira ya yi ga gwamnatin Shugaba Jonathan ta hanzarta kamo masu kisa wannan ta’asa don fuskantar shari’a, inda ya ce ya kadu tare da bakin ciki kan asarar dimbin rayukar da aka yi a ranar Litinin din.
Ban Ki-moon ya kara da cewa Majalisar dinkin Duniya tana goyon bayan gwamnati domin kawo karshen rashin tsaro a Najeriya. Ya yi Allah wadai da kashe-kashen da ake aiwatarwa a kan al’ummar Arewacin Najeriya, inda ya bukaci a hanzarta kamo masu shiryawa da aiwatar da hare-haren don hukunta su.