Obama ya bukaci ’yan Najeriya su guji tarzoma lokacin zabe

Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya yi kira ga ’yan Najeriya da kar su yarda zaben gobe (Asabar) yabi sahun wadanda suka gabace shi wajen sukurkucewa. Shugaban ya yi wannan kiran ne a jawabi ranar Litininin, inda ya ce samun zabe nagari shi ne abin da zai kawo karshen kungiyar Boko Haram, wanda ya raba […]

Obama ya bukaci ’yan Najeriya su guji tarzoma lokacin zabe
Obama ya bukaci ’yan Najeriya su guji tarzoma lokacin zabe

Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya yi kira ga ’yan Najeriya da kar su yarda zaben gobe (Asabar) yabi sahun wadanda suka gabace shi wajen sukurkucewa.

Shugaban ya yi wannan kiran ne a jawabi ranar Litininin, inda ya ce samun zabe nagari shi ne abin da zai kawo karshen kungiyar Boko Haram, wanda ya raba miliyoyin yan Najeriya da muhallansu.
Ya ce: “Ina fata shugabannin siyasa musammam ’yan takara za su ja kunnen magoya bayansu, kuma su kwana da sanin cewa tayar da tarzoma ba ta da gurbi a dimukradiyya.”
A karshe ya bukaci ’yan Najeriya da masu jefa kuri’a da su yi kunnen kashi ga duk wani dan siyasar da zai bukace su da su tada tarzomar zabe, ya ce, “muddin aka yi zabe mai adalci to wajibin ’yan kasa ne su tabbatar an samu zaman lafiya koda ko waye ya samu nasara.”
A wani labarin kuma a jiya Alhamis ne Fira ministan Birtaniya, Dabid Cameron , ya yi kira ga shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan da ya yi duk abinda zai yi domin ganin an gudanar da zaben gobe Asabar. Mista Cameroon ya ce duk wani abu, koma baya ga haka, zai iya jefa kasar cikin hadari, da kuma zai shafi kimarta a idon duniya. A wata wasikar da ya aike wa Shugaban Najeriyar, firaministan ya nuna mahimmancin gudanar da zabe ta hanyar dimukradiyya a nahiyar Afirka.