Obama ya ce babu irin Buhari uku a Afirka – Rochas Okorocha

A ziyarar aiki da Shugaba kasa Muhammadu Buhari ya kai Amurka Aminiya ta samu zantawa da Gwamnan Jihar Imo Owelle Rochas Anayo Okorocha da ke cikin ayarin Shugaban kasar, inda ya ce Shugaban Amurka Barack Obama ya ce a Afirka babu irin Buhari uku. Ga yadda hirar ta kasance: Aminiya: Kana iya cewa ziyarar da […]

Obama ya ce babu irin Buhari uku a Afirka – Rochas Okorocha
Obama ya ce babu irin Buhari uku a Afirka – Rochas Okorocha

A ziyarar aiki da Shugaba kasa Muhammadu Buhari ya kai Amurka Aminiya ta samu zantawa da Gwamnan Jihar Imo Owelle Rochas Anayo Okorocha da ke cikin ayarin Shugaban kasar, inda ya ce Shugaban Amurka Barack Obama ya ce a Afirka babu irin Buhari uku. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Kana iya cewa ziyarar da kuka kawo kwalliya ta biya kudin sabulu?

Rochas: Na farko dai wannan ziyara abin farin ciki ne a gare mu, ba gwamnoni kawai ba duk ’yan Najeriya da masoyan Najeriya, domin abin da a da ba mu taba tsammani ba ne, amma sai ga shi ya faru. Yadda aka karbi Shugaban kasarmu abin farin ciki ne da ba mu taba tsammani za mu gani ba, domin da muka taso daga Najeriya muka iso Amurka mun dauka yadda aka saba yi ne za a yi mana, amma abin farin ciki abin mamaki an karbe hannu bibbiyu, abin da ba mu yi zato za a yi ba, duk an yi, sun yi mana kalamai da maganganu masu dadi, a takaice Amurka ta yin shirin hacuwa da Najeriya, domin ganin an canja halin da ake ciki. Wannan duk cikin soyayyar da suka nuna wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne, wanda hatta shi Obama da kansa ya ce ba irin Shugaba Buhari guda uku a Nahiyar Afirka, domin shi mutum ne mai gaskiya kuma yana kyamar yadda shugabannin ke cutar jama’arsu. Bayan haka mun gana da mutanen duniya, su ma sun ba mu goyon bayansu dari bisa dari. Kuma mun gana da Mataimakin Shugaban Amurka, Joe Bidden da Sakataren Harkokin Wajen Amurka, John Kerry ga su nan dai duk manyan Amurka da ka sani mun zauna da su kuma kalaman da suka yi mana masu dadi ne. Kuma ni a zatona sun yi wannan ne domin shi kansa Shugaba Buhari ba wai don mutanen Najeriya ba. Don haka yanzu mu san daga nan zuwa gaba za a samu sabuwar Najeriya a fannoni daban-daban, domin canjin nan da ake ta magana, na san nan ba da dadewa ba za a gan shi.
Aminiya: To, mutanen Jihar Imo wane canji za su gani nan gaba game da wannan ziyara?
Rochas: Da ka san na yi shekara hudu, yanzu kuma an sake ba ni wata damar yin wasu shekara hudu, da farko dai na yi musu alkawarin cewa zan mayar da ilimi kyauta daga firamare zuwa sakandare daga nan har zuwa jami’a. Kuma duk wadannan alkawura da na yi musu na cika su, haka kuma na ce zan gina asibitoci 27, kowannensu mai gado 100 kuma na yi. Haka makarantu mun gina adadin da ya kai dubu uku da 50. Dukkan wadannan makarantu gidan sama ne, domin da ana cewa yaran talakawa ba za su samu zuwa makaranta ba, na ce wannan ba zai yiwu ba lokacina, bayan na samar da wannan ne na ce a wadannan shekara hudu zan tabbatar an samar wa matasa da aikin yi. Za mu tabbatar mun wadata kowa da aiki ta yadda idan muka same ka a kan hanya ba ka aikin komai sai mu kama ka, wato shirin namu a Ingilishi ana kiransa YOUTH MUST WORK. Wannan ya sa muka ce za mu kafa masana’antu ta yadda kowa zai amfana da aikin yi. Wani bangare da za mu samar da aikin yi, shi ne noma domin daga yanzu duk filin da muka ga mai shi bai noma ba, to, gwamnati za ta karbe shi a matsayin aro, idan muka gama noma sai mu mayar maka da filin. Don haka mutanen Jihar Imo sun san cewa tuni muka shiga sabon yayi. Idan ka dubi batun mai yanzu a kasar nanakwai matsala, kai matsaloli ma zan ce, domin idan ka lura yanzu kudin mai ya sauka kasa kuma ko baya ga wannan duk an bi ana sace man, ba mu samun abin da muke samu kamar da domin duk wasu sun sace mai yawa, shi ya sa muka ce bari mu duba shin ciki gida me za mu iya yi domin taimakon kanmu. Shi ya sa muka ce na daya za mu koma noma mu samar da masana’antu ta yadda matasa za su fara aikin yi. Wannan yana cikin alkawarin da na yi kuma insha Allahu zan cika, musamman da yake za mu tattauna da masu masana’antu domin su je jiharmu su kafa irin masana’antun da suke da su.
Aminiya: Wasu ’yan Najeriya na kiran Shugaba Buhari da Baba Mai Tafiyar Hawainiya (Baba Go Slow) mene ne ra’ayinka kan wannan suna?
Rochas: To ka san dai halin ’yan Najeriya, wani lokaci idan ka ji kalamansu sai ka ce lamarin ’yan Najeriya sai a yi shiru, su so suke yi komai a yi shi da zafi-zafi ba su son a ce a kwana zuwa gobe a ci gaba da maganar da aka ce za yi, su dai kome cikin sauri suke son a yi shi, so suke a ce Shugaba Buhari na hawa a ce duk matsalolin Najeriya an magance su kawo yanzu. Shi ya sa suke ganin abubuwa ba su tafiya yadda suke zato. Amma abin da ya kamata shi ne ya dace a yi komai cikin tsanaki, domin ba sai an yi ba a zo a yi kuskure a sake shiga cikin wani halin damuwa. Ka lura fa shekara 16 ana mulkin PDP kuma da APC ta ci zabe kamata ya yi a yi mika bayanan harkokin mulki amma har yau ba a mika wasu bayanan ba.
Aminiya: Kana nufin ba su mika muku takardun mika mulki ba?
Rochas: Shi ya sa ya kirawo mutum 18 da suka san kan aiki daga na gwamnati zuwa na masu zaman kansu har da banki ya tattaro ya hada su ya ce su duba shin daga ina ya kamata su fara. Ya ce su duba me ke kowace ma’aikata kuma nawa ake binmu bashi, nawa muke bi, kuma menene matsalar kasar, domin ba wata takardar da aka ba shi na daga ina zai faro. Za ka nada ministoci ne ba ka san irin aikin da za ka ba su ba? Shi ya sa yake son ya dauki lokaci ya duba tsarin da zai bi domin yin aiki bisa tsari da ka’ida da yadda ya dace a yi shi.
Aminiya: Mene ne ra’ayinka kan takaddamar da ake yi a banagarori biyu na majalisar dokoki ta kasa?
Rochas: Wannan siyasa ce tsakanin Jam’iyyar APC kuma Shugaba Muhammadu bai son ya ce a ba wannan wani mukami kaza a ba wancan wani abu. Shi ya sa ya ce ba zai sa baki ba, duk abin da kuka ga dama ku yi, wannan shi ne dalilin wannan rikici.
Aminiya: Wasu na ganin hakan da ya yi ya sa aka samu wannan matsala.
Rochas: Haka ne, amma ya kamata a yi haka domin idan ana dimokuradiyya to abin da hakan ke nufi ku yi yadda kuka ga dama muddin dai bai saba wa doka ba. Ku zabi wanda kuke so, ko kuke ganin ya dace, ba sai an nuna muku ba, to amma kuma sai a nan aka samu matsala cikin wannan magana shi ne sai ’yan jamiyyar tamu suka tashi domin neman shugabancin Majalisar Wakilai da ta Dattawa, kuma duk da haka sai ya kasance a cikin ’yan Majalisar Dattawa jam’iyyarmu na da sanatoci 59, ita kuma jam’iyyar adawa ta PDP tana da 49, ke nan goma ke tsakaninmu, to da aka samu mutum biyu suna neman shugabancin majalisar, sai matsala ta kunno kai a jam’iyyar tamu domin su biyun za su raba kuri’arsu don haka idan wani ya taso daga PDP ya yi takara, zai zama shugaban majalisar, shi ya sa sai Sanata Bukola Saraki ya yi sauri ya dauki Sanata Ike Ekweremadu ya zama mataimakinsa domin samun kuri’ar ’yan PDP. To a nan ba za a ce wane ya yi laifi ba, ko wane bai yi laifi ba. Shi kuma maigidan da ya ba su izini ya yi ne domin a bi ka’idar dimokuradiyya, sai abin ya koma wani abu wanda idan ba mu yi hankali ba za mu shiga uku domin ba za mu samu shugabancin majalisar ba, kuma muna da Shugaban kasa haka bai dace ba, amma mu gwamnonin APC mun shiga cikin maganar domin a yi gyara.
Aminiya: To yawanci jihohi suna kukan cewa ba su iya biyan albashi ina matsayin Jihar Imo cikin wannan batu?
Rochas: Da zafinta gaskiya.
Aminiya: Kana nufin ba kudi ke nan?
Rochas: Ni ba zance ba kudi ba, akwai kudi a kasarmu
Aminiya: Wasu ba su biyan albashi a halin yanzu…
Rochas: Wannan haka ne domin kudin ba su isa ba ne.
Aminiya: To yanzu kai a jiharka ana biyan albashi?
Rochas: Ma’aikata suna bin mu wata daya wasu wata biyu wasu kuma uku amma dai bai wuce wata uku ba, domin abin ba mu yi tsammani zai faru haka ba, domin wata rana sai ka tashi abin da kake samu ba za ka samu ko rabin haka ba. Wannan ya sa muka fara duba wani bangare domin wata rana idan ba kudin man yaya za mu yi, shi ya sa na kawo maganar noma, domin maganar man ta zame mana rudu kwarai da gaske shi ya sa Shugaban kasa ke neman hanyar da za a samu kudin shiga daban-daban ba wai daya kawai ba, don haka idan wannan ya samu wannan matsala za ta kau.
Aminiya: Mene ne ra’ayinka game a gidan Rediyon Biyafara, wanda ake cewa yana watsa labaran raba kan mutane?
Rochas: Rediyon Biyafara ina ji ana fada, amma ban san da shi ba, kuma ba wani shugaban Ibo na kwarai da zai goyi bayansa, tunda mutane ne suna magana ban san mene ne nufinsu ba. Wadanda suka fara wannan abin ba mu sansu ba kuma za mu ce ga wani shugaban Ibo da yake bayansu ba, ba mu san ko wane ne ke bayansa ba, muna kallonsa ne kamar maganar sace mutane a yi garkuwa da su ko Boko Haram. Kuma an kai kara ga Gwamnatin Tarayya, Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talabijin ta kashe gidan rediyon gaba daya ba a jin su yanzu, ina godiya da aka shiga cikin maganar da zafinta aka dakatar da shi.
Aminiya: Ku yanzu kuna wani yunkuri na ce wa mutanenku su yi watsi da gidan rediyon?
Rochas: Ina fada maka ba wanda yake cikin wannan batu na gidan rediyon, mun fada wa mutane su fita hanyarsu ba masu son zaman lafiya ba ne ’yan iska ne suke abinsu ba mu san da su ba. Mun ce mutane su kyale su kada wani ya sa musu baki har ya fara numfashi kamar Boko Haram a shiga wata matsala ta daban.
Aminiya: Shin yaya kuke kallon Shugaba Muhammadu Buhari?
Rochas: Shugaba Muhammadu Buhari mutum ne da zan ce wanda lokacinsa ya zo, kuma Allah Yana goyon bayansa, domin abin da ya faru a zaben da ya kawo Shugaba Buhari kan mulki babban abin mamaki a nan kasar a ce mutumin da ke kan karagar mulki an kada shi. Wannan ba wanda ya taba tunanin zai faru, domin Jonathan yana da sojoji da ’yan sanda da kudi da duk abin da mai mulki ke da shi, amma aka kada shi. Kuma Muhammadu Buhari ba ya da komai sai Allah kuma Allah Ya tsaya a bayansa, domin shi mai tsoron Allah ne, fatarsa ya yi aiki ya bar tarihi nagari. Ba mai kwadayi ba ne fatarsa koyaushe yaya za a yi a samu ci gaban Najeriya, ba ya son ya ji batun cin hanci da rashawa kuma abin duniya bai dame shi ba. Mutumin da ya yi Ministan Mai, ya yi Gwamna amma ba wani abu babba da za ka nuna ka ce nasa ne kai ka san wannan zabin Allah ne, sai dai mu yi ta yi masa addu’a.