Obama ya kai ziyara wani masallaci a Amurka
A shekaranjiya Laraba ne Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya kai ziyara wani masallaci a birnin Baltimore da ke Jihar Maryland.Shugaban ya kai ziyarar a wani yunkuri na kwantar da hankulan Musulmi game da kallon da ake ci gaba da yi musu na ’yan ta’adda.A jawabinsa ya bayyana cewa duk wanda ya takali Musulunci kamar […]
A shekaranjiya Laraba ne Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya kai ziyara wani masallaci a birnin Baltimore da ke Jihar Maryland.
Shugaban ya kai ziyarar a wani yunkuri na kwantar da hankulan Musulmi game da kallon da ake ci gaba da yi musu na ’yan ta’adda.
A jawabinsa ya bayyana cewa duk wanda ya takali Musulunci kamar ya takali saura addinai ne. Har ila yau, ya ce mai neman takarar shugabancin kasar karkashin Jam’iyyar Republican, Donald Trump da kuma sauran ’yan takara ba su da wata hujja ta dora wa Musulmi karar tsana.
Daga nan ya ce: “Idan aka takali wani addini, akwai nauyi da ya rataya a wuyanmu wato mu tashi tsaye don yin magana.”
A farkon watan Disambar bara ne Mista Trump ya yi kira da a haramta wa Musulmi shiga Amurka bayan wani hari da wasu Musulmi mata da miji suka kai a Jihar California, inda suka hallaka mutane 14.
A yayin ziyarar, Shugaba Obama ya cire takalman da ke kafarsa kamar yadda Musulmi suke yi idan za su shiga masallaci. Hakazalika, bayan shigarsa wani mutum da wata mata sun karanta wata aya daga cikin Al-kur’ani wadda take koyar da hakuri da juna.
Kodayake, Obama mabiyin addinin Kirista ne, amma a jawabinsa ya ba da tarihin addinin Musulunci a Amurka. Inda ya ce daya daga cikin wadanda suka kafa kasar wato Thomas Jefferson ya ambaci Musulmi lokacin da yake bayani game ’yancin Amurkawa kan zabar addinin da suke so.
“Amma masu adawa da Jefferson sun ce ya fadi hakan ne saboda shi mabiyin addinin Musulunci ne a boye. Ashe ba kaina aka fara irin wannan zargin ba,” inji Shugaba Obama wanda shi ma wasu da dadewa suke masa zargin kasancewa Musulmi a boye, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya bayyana.
Har ila yau, Shugaban ya bukaci wasu sojojin Amurkan Musulmi da ke tare da shi su mike tsaye da kuma Ibtihaj Muhammad (wadda ita ce Musulma ta farko daga Amurka da za ta fafata sanye da hijabi a wasannin Olympic na bana a birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil.)
Hakazalika, ya bayyana wa, wasu dimbin yara da suka taru a harabar masallacin don kallon jawabinsa ta wani babban akwatin talabijin, cewa su ma wata rana za su iya zama shugaban kasar Amurka. Ga alama wannan martani ne ga mai neman takarar shugabancin kasar karkashin Jam’iyyar Republican, Ben Carson, wanda a watan Satumbar bara, ya ce ba zai taba goyon bayan wani Musulmi ya zama shugaban Amurka ba.
A karshe ya nanata cewa: “Musulmi sun cancanci kasancewa a Amurka.”