Obama ya kammala ziyararsa a Cuba

Ranar Talata ce ranar karshe ta ziyara mai cike da tarihi da Shugaban Amurka Barack Obama ya kai  kasar  Cuba.Shugaban ya ce ya je Cuban ne domin kammala sasanta rashin jituwan da yayi ke tsakanin kasar da Amurka, tun daga lokacin yakin cacar-baka.A jawabin da ya gabatar wanda gidan talabijin na Cuban ya yada, Mista […]

Obama ya kammala ziyararsa a Cuba
Obama ya kammala ziyararsa a Cuba

Ranar Talata ce ranar karshe ta ziyara mai cike da tarihi da Shugaban Amurka Barack Obama ya kai  kasar  Cuba.
Shugaban ya ce ya je Cuban ne domin kammala sasanta rashin jituwan da yayi ke tsakanin kasar da Amurka, tun daga lokacin yakin cacar-baka.
A jawabin da ya gabatar wanda gidan talabijin na Cuban ya yada, Mista Obama ya ce lokaci ya yi da za a samu sauyin dangantaka tsakanin Amurka da Cuba.
Har ila yau, ya bukaci jama’ar Cuba da ta rungumi sauyi, sannan ta dubi gaba da fata na gari.
Mista Obama ya ce Amurka za ta mutunta banbance-banbance da ke tsakanin kasashen biyu, kuma ba za ta tilasta wa Cuban aiwatar da sauye-sauye ba, kamar ya BBC ta bayyana.
Shugaba Obama da takwaransa na Cuban Raul Castro sun yi shiru na minti daya don nuna jimamin mutanen da suka mutu a hare-haren da aka kai birnin Brussels.