Obama ya ware Dala miliyan 500 don yakar Ebola
Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya ce kasarsa za ta taimaka da Dala miliyan 500 da kuma dakaru 3,000 wadanda za a aika yankunan da annobar Ebola tafi kamari don shawo kan cutar.Shugaban ya ce Amurka ta shirya tsaf don jagorantar yaki da annobar, sai dai kuma ya bayyana cewa cutar wadda tayi kamari a […]
Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya ce kasarsa za ta taimaka da Dala miliyan 500 da kuma dakaru 3,000 wadanda za a aika yankunan da annobar Ebola tafi kamari don shawo kan cutar.
Shugaban ya ce Amurka ta shirya tsaf don jagorantar yaki da annobar, sai dai kuma ya bayyana cewa cutar wadda tayi kamari a Yammacin Afirka tana neman gagarar kundila.
A lokacin da yake bayyana fadada matakan yaki da cutar, ranar Talatar da ta gabata, ya ce Amurka za ta kafa cibiyoyinn kula da masu dauke da cutar da wuraren kebe su da kuma bai wa ma’aikatan lafiyar da za su duba su irin horon da ya kamata. Har ila yau, kasar za ta taimaka wajen inganta fanin sadarwa da sifuri a yankunan.
A makon jiya ne dai Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), ta ce cutar ta yi ajalin fiye da mutum 2,400 cikin 4,784 da suka harbu da ita, a yankin Afirka ta Yamma tun farkon fara bullar ta a watan Fabrairun bana, a kasar Guinea.