Obama ya yi Allah-wadai da kisan ‘yan jarida
Shugaban kasar Amurka ya yi Allah-wadai da kisan wasu ‘yan jarida biyu, wadanda aka kashe shekaranjiya Laraba a Jihar birginia ta kasar Amurka lokacin da suke daukar wata hira ta talabijin.Wani hoton bidiyo da aka sa a shafin YouTube ya nuna wata ‘yar jarida ta fara hira da wani bako, kafin a ji karar harbin […]
Shugaban kasar Amurka ya yi Allah-wadai da kisan wasu ‘yan jarida biyu, wadanda aka kashe shekaranjiya Laraba a Jihar birginia ta kasar Amurka lokacin da suke daukar wata hira ta talabijin.
Wani hoton bidiyo da aka sa a shafin YouTube ya nuna wata ‘yar jarida ta fara hira da wani bako, kafin a ji karar harbin bindiga har sau takwas, sai kyamarar ta fadi kasa kuma ana iya jin ihu, kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta bayyana.
Gidan talabijin din da ‘yan jaridar kewa aiki, WDBJ7, ya ce wadda ke hirar Alison Parker da mai daukar mata hoto, Adam Ward dukkansu sun mutu a lamarin da ya faru a rukunin shaguna na Bridgewater da ke garin Moneta a yankin karamar hukumar Bedford. Zuwa lokacin hada wannan rahoton jami’an tsaro sun ce wanda ake zargi da kisan ‘yan jaridan ya harbe kansa, amma suna ci gaba da bincike a kan batun.