Obama zai dakile bazuwar bindigogi a Amurka
Shugaban kasar Amurka Barrack Obama ya zubar da hawaye lokacin da yake jawabi kan yadda iznin mallakar bindiga ke ci gaba da lakume rayukan Amurkawa.Al’amarin y afaru ne lokacin da yake wa Amurkawa jawabi a fadarsa da ke White House, wanda ya samu halartan ’yan uwan wadanda suka yi hasarar wasu nasu sakamakon harbin bindiga […]
Shugaban kasar Amurka Barrack Obama ya zubar da hawaye lokacin da yake jawabi kan yadda iznin mallakar bindiga ke ci gaba da lakume rayukan Amurkawa.
Al’amarin y afaru ne lokacin da yake wa Amurkawa jawabi a fadarsa da ke White House, wanda ya samu halartan ’yan uwan wadanda suka yi hasarar wasu nasu sakamakon harbin bindiga a lokuta daban-daban a baya.
Jawabin Shugaba Obama mai sosa rai ya caccaki ’yan Majalisar Dokokin kasar musammam wadanda suka ki amince da yi wa dokar mallakar bindiga kwaskwarima. Ya ce Amurkawa su daure a dauki matakin da suka dace wajen mallakar bindiga.
Ya ce a kowace shekara kusan Amurkawa dubu 30 ne ke mutuwa sakamakon harbin bindiga ta hanyoyi kisan kan mai uwa da wabi, ko kuma masu kashe kansu, ko kuma tashe-tashen hankula a wajen taro da dai sauran su.
Har ila yau, shugaban ya ce Amurka ce kasar da ta ci gaba, amma kuma take huskantar hadarin salwantar rayuka ta harbin bindiga, abin da ba a gani a sauran sassan duniya musammam a cikin kasashen da suka ci gaba.
Shugaban ya bayyana matakai da gwamnati za ta dauka abin da ya kira aiki da hankali. Ya ce zai yi amfani da ikonsa na shugaba mai cikakken iko ba tare da amincewar majalisar dokokin kasar ba, wadda da ta yi ta wa yunkurin kafar angulu wajen yiwa dokar kwaskwarima musammam ’yan jam’iyyar Republican.
Wasu daga cikin matakan da shugaban ya bayyana zai dauka sun hada da tantancewa mai tsauri ga dillalan bindiga su samu karin lasisi. Har ila yau, za a bi dokokin mallakan bindiga sau da kafa sabanin abin da ake da shi yanzu.
Wannan batu ya janyo muhawara tsakanin Amurkawa kamar yadda wasu suke cewa matakan ba wasu tasiri za su yi ba, kuma tamkar karan tsaye ne ga gyaran dokar da majalisar ke yi wanda ya kai matakin karatu na biyu a zauren majalisar.