Obasanjo da Buhari na yunkurin kafa gwamnatin rikon kwarya – Gwamnati
Ministan Harkokin ’Yan sanda, Jelili Adesiyan, ya zargi tsohon Shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo da dan takarar Shugaban kasa na Jam’iyyar APC Manjo Janar Muhammadu Buhari da shirye-shiryen kafa gwamnatin rikon kwarya a kasar nan.Ministan ya yi wannan zargi ne a Legas wajen kaddamar da wani littafi mai suna, ‘Watch the Watcher,’ da wani dan […]
Ministan Harkokin ’Yan sanda, Jelili Adesiyan, ya zargi tsohon Shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo da dan takarar Shugaban kasa na Jam’iyyar APC Manjo Janar Muhammadu Buhari da shirye-shiryen kafa gwamnatin rikon kwarya a kasar nan.
Ministan ya yi wannan zargi ne a Legas wajen kaddamar da wani littafi mai suna, ‘Watch the Watcher,’ da wani dan kare ’yancin jama’a mai suna Yinka Odumakin, ya rubuta don mayar da martani ga littafin Obasanjo da ya jawo cece-kuce mai suna ‘My Watch’.
Ministan ya ce “Da dama wadanda suke cikin APC ’yan PDP ne da aka bata musu, kuma ba su da tagomashi a idon jama’a, saboda ba su samu nasara ba, inda suka koma zafafa harkokin siyasa. Sun ce za su kafa tasu gwamnati idan suka fadi a zabe. Kuma na riga na fada wa Sufeto Janar na ’Yan sanda da Hukumar SSS su kama duk wanda ya fadi irin wannan mugun kalami da magana mai tayar da hankali.”
“Tuni Obasanjo yake shirin kafa gwamnatin rikon kwarya tare da Buhari. Amma za jefa kuri’a kuma za mu yi aiki da duk wanda ya ci zaben,” inji Ministan.
Ya kara da cewa Obasanjo ya dauki Jonathan a matsayin Mataimakin Shugaba Umaru ’Yar’aduwa ne bisa fatar ya rika juya shi, amma sai bai samu nasara ba.
Ministan ya ce, “Ya dora Shugaban kasa marar lafiya, kuma a lokacin da muke yawon kamfen din Shugaban kasa shi (’Yar’aduwa) kusan kullum yana Jamus wajen jinya. Kuma a lokacin da mutane da dama ke kamun kafa don hawa kujerar Mataimakin Shugaban kasa, Obasanjo ya dauki dattijo, Goodluck Jonathan, wanda bai da wani karfi a siyasa ta yadda zai rika juya shi. Sai dai abin takaici ga Obasanjo, Ubangiji Yana da nasa tsari mafi alheri, sai Jonathan ya ki yarda a juya shi. Obasanjo kamar yadda aka san shi yanzu yah ade kai da Bola Tinubu da Atiku Abubakar su kwace mulki, Tinubu zai yi masa shigar sauri saboda mu mutanen Osun masu basira ne. Ku tambayi Tinubu, shi dan uwan ne jiharmu daya. Ya fito ne daga Iragbiji, ni kuma daga Ode-Omu.”
Sai dai Daraktan Sadarwa na Kwamitin Yakin Neman Zaben Janar Buhari, Mista Dele Alake, ya ce abin dariya ne wani ya ce Buhari yana shirin kafa gwamnatin rikon kwarya a lokacin da Buharin yake fafatawa a takarar Shugaban kasa.
Ya ce, “Ina tabbatar wa ’yan Najeriya PDP ta rasa amsar da za ta bayar ne kan dimbin matsalolin da ta jefa Najeriya a ciki, shi ya sa ta koma ga kamfe din bata suna da cin mutunci. Idan Buhari yana shirye-shiryen kafa gwamnatin rikon kwarya, me zai sa ya tsaya takarar Shugaban kasa. Ina jin kwakwalwarsu ta daina aiki ne.”
Ya kara da cewa, “Zaben Buhari ne kawai zai magance mugun halin da Najeriya ta fada. Domin sai mutum mai tarbiyya irin Buhari ne zai fitar da kitse daga wuta.”