Obasanjo: Kishin kasa ko kishin kai?

daya da daya yau a kasar nan ba wani shugaba da ya amsa sunan shugaba a cikin harkokin mulkin dimokuradiyyar nan da ya kai tsohon Shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo zama Karan kada miya, cikin bayyana irin abin da ransa ya yi masa dadi daidai ko ba daidai, bisa ga irin yadda masu mulkin kasar […]

Obasanjo: Kishin kasa ko kishin kai?
Obasanjo: Kishin kasa ko kishin kai?

daya da daya yau a kasar nan ba wani shugaba da ya amsa sunan shugaba a cikin harkokin mulkin dimokuradiyyar nan da ya kai tsohon Shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo zama Karan kada miya, cikin bayyana irin abin da ransa ya yi masa dadi daidai ko ba daidai, bisa ga irin yadda masu mulkin kasar a yau suke tafiyar da al`amurran mulkinsu. Ga `yan kasa da ba su san tarihin tsoma bakin tsohon shugaba Obasanjo yake yi, tun bayan lokacin da ya bar mulki a ranar 01-10-1979, da ya mika wa gwamnatin farar hula a inuwar jam`iyyar NPN, ta su Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari mulki, sai su yi zaton sai bayan da ya bar mulkin shekaru takwas na farar hula (1999 zuwa 2007) din nan ya fara haka.
Alhali kuwa ko kusa ba haka batun yake ba, tarihi ya tabbatar da cewa tunda ya bar mulki a karon farko a shekarar 1979, har ya dawo a zaman shugaban farar hula, da rana daya Cif Obasanjo bai taba rufe bakinsa ba a kan gwamnatocin da suka biyo bayansa ba, na mulkin soja ne ko na farar hula. Ita kanta Gwamnatin Alhaji Shehu Shagari da `yan kabilar Cif Obasanjo, ta Yarbawa, suka rinka afkawa akan bai kyauta masu ba, da ya mika wa Alhaji Shagari mulki, alhali ga dan kabilarsa Cif Obafemi Awolowo, na jam`iyyar UPN, da ya zo na biyu a cikin wancan zabe, tunda a tunaninsu a lokacin yana da ikon ya murde zaben.
Gwamantin tsohon shugaban kasa ta Janar Ibrahim Babangida kuwa ta shekaru takwas 1985 zuwa 1993, ba irin sukar da ba ta sha ba daga Cif Obasanjo, musamman akan irin yadda ta rinka jan kafa wajen mayar da mulki hannun farar hula da irin yadda ta fito karara ta nuna tana son ta gaji kanta da sunan“TAZARCE,” da irin yadda ta soke zaben 12 ga watan Yunin 1993, wanda aka kyautata zaton Cif Moshood Abiola, dan kabilar Yarbawa ya lashe sa. Ta kai fagen a lokacin da sukar ta yi suka akan  gwamnatin ta Babangida sai da Cif Obasanjo ya bayyana gwamnatin da cewa “Idan ta ce da `yan kasa Barka da asuba, to, su daga labulan tagarsu su duba, don su iya tantance lokacin da ake ciki kafin su mayar ma ta da sallama. Gwamnatin Janar Sani Abacha da ta yi mulkin shekaru biyar (1993 zuwa 1998) ne kadai, da ta gaji da soke-sokensa ta taka masa burki, inda a ranar Juma`a 17-03-1995, ta kama shi, shi da Janar Shehu Musa `Yar`aduwa da wasu jami`an sojoji da na farar hula da zargin laifin yunkurin juyin mulki, daga bisani kuma ta same su da laifi, inda ta yanke musu hukuncin kisa. Roko da kiraye-kirayen jama`a da kungiyoyi na ciki da wajen kasar nan, ga gwamnatin tarayya suka sanya daga bisani gwamnatin ta canja hukuncin zuwa na daurin rai-da- rai, ga manyan mutanen biyu.
Bayan mutuwar Janar Abacha ne a ranar 08-06-1998, kuma zuwan gwamnatin Janar Abubakar Abdussalami, da hadin bakin wasu `yan Arewa suka sa aka yafe wa Cif Obasanjo, sannan kuma suka ba shi takarar neman shugabancin kasa a inuwar jan`iyyar PDP, duk da aniyarsu na gyara barnar da suka yi ta soke zaben 12 ga watan Yuni. Cif Obasanjo ya kwantar da kansa a zangonsa na farko, amma a zango na biyu ya mike kafafunsa, ta yadda kusan dukkan `yan Arewar da suka taimaka masa ya hau mulkin, sai da ya yarfar da su. Samun wannan dama ta sanya a shekarar 2007, da ya  kasa cimma burinsa na yin “TAZARCE,” shi kadai ya dauko Gwamnan Jihar Katsina, marigayi Alhaji Umaru Musa `Yar`aduwa da shugaba Dokta Goodluck Jonathan a lokacin yana Gwamnan Jihar Bayelsa ya nada su `yan takarar neman shugabancin  kasa da mataimaki bi-da-bi, suka kuma yi nasara.
Allah cikin ikonSa sai ya karbi ran shugaba `Yar`aduwa a watan Afrilun 2010, inda mataimakinsa Dokta Jonathan ya ci gaba da mulki aka yi zabe bayan shekara guda shugaba Jonathan ya sake samun nasara. Dukkan shugabannin biyu ’Yar`adu da Jonathan, duk da Obasanjo ya yi sanadin zuwansu kan karagar mulki, amma da rana daya Cif Obasanjo bai taba sassauta musu ba wajen sukar yadda suke tafiyar da gwamnatinsu. Alal misali an taba jin Cif Obasanjo yana bayyana shugaba `Yar`aduwa da cewa tamfar Kurma yake, don wai ba ya jin maganar da ake masa. Inda marigayi `Yar`aduwa ya ci ribarsa ke nan bai kula shi ba, kuma bai bari ba makarrabansa su rinka ba Obasanjo amsa, sannan kuma Allah Ya yi masa gajeren kwana,
Yanzu maganar da ake, duk damar da Cif Obasanjo ya samu sai ya soki Gwamnatin Jonathan, musamman karatowar zabukan 2015. Koda a cikin `yan kwanakin nan a karo biyu cikin mako daya ya soki Gwamnatin Shugaba Jonathan. Sukar farko, ya yi ta a wajen bikin nunin al`adun gargajiya da littafai na Are da aka yi a Abeokuta, inda ya bayyana aikace-aikacen gwamnatin tarayyar da cewa ba su kai mizanin da za a yaba ba. Wata sukar ta baya-bayannan akan mulkin shugaba Jonathan, ita ce Shugaba Jonathan ya dauki shekaru uku kafin ya fahimci me ke akidar `yan kungiyar Jama`atul Ahlis Sunnah Lidda`awaiti Wal jihad da ake yi wa lakabi da Boko Haram. Akidar da ya ce ta gauraya da karancin ilmi koma rashinsa kwata-kwata, wadda yake sa wa `yan kungiyar kuskuren fahimtar koyarwa ta Al`kur`ani da sunnar Manzo SAW. Cif Obasanjo ya bayyana Talauci da rashin ayyukan yi da rashin adalci irin na masu mulkin wannan zamanin da shaye-shayen miyagun kwayoyi da bazuwar kananan makamai a hannun jama`a da kasa iya tafiyar da mulki cikin kamanta gaskiya da adalci da uwa uwa cin hanci da rashawa da suka mamaye kusan dukkan sassan rayuwar al`umma da makamantan matsaloli a matsayin abubuwan da suke addabar kasar nan a halin yanzu, wadanda ya ce gwamnati Jonatahan din ta gaza shawo kansu.
Bayan wadannan soke-soke ga gwamnatin tarayya, wasu daga cikin gwamnonin jam`iyyar PDP su biyar da suka hada da gwamnonin jihohin Jigawa Alhaji Sule Lamido da Gwamnan jihar Neja Dokta Ma`azu Babangida suka ziyarce Cif Obasanjo da aniyar su lallashe shi, ya mayar da wukar a kubenta. Kodayake gwamnonin bayan taron sun shaida wa manema labarai cewa batutuwan da suka tattauna da Cif Obasanjo, batutuwa ne na batun kasa, musamman tabarbarewar matakan tsaro. Amma daga bisani ta bayyana, rokon Cif  Obasanjo suka je yi, kamar yadda sabon Gwamnan Jihar Ekiti Mista Ayodele Fayose, ya fada wa manema labarai cikin fushi akan irin rashin dattakon Cif Obasanjo, shugaban da ya bayyan da cewa muddin ba ra`ayinsa za a bi ba, to kuwa ba wani mai sahihin ra`ayi.
Kome dai ake ciki, tsakanin Cif Obasanjo da shugaba Jonatahan da Jam`iyyarsu ta PDP, da kuma karatowar zabubbukan 2015, yanzu ta bayyana Cif Obasanjo ya zama “Karan kada miya” a fagen siyasar kasar nan, ta yadda dukkan manyan jam`iyyun kasa biyu PDP (jam`iyyarsa ta asali) da sabuwar babbar jam`iyyar adawa ta APC, a kullum makarrabansu suna Safa da Marwa gidan Cif Obasanjo. Wannan ke nan yana nufin Obasanjo yana yin haka ne don kishin kasa ko don kishin kansa? Allah Ka ba mu ikon zaben shugabanni na gari tun daga sama har kasa amin summa amin.