Obasanjo ya gargadi Buhari kada ya tsaya takara a 2019
Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya gargadi Shugaba Buhari da kada ya tsaya takarar shugabancin kasa a zaben mai zuwa na shekarar 2019 kamar yadda Premium Times ta ruwaito. A wata takarda ta musamman mai dauke da shafi 13 wadda Obasanjo ya fitar a yau din nan (Talata), ya ce Shugaba Buhari bai yi abin […]

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya gargadi Shugaba Buhari da kada ya tsaya takarar shugabancin kasa a zaben mai zuwa na shekarar 2019 kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
A wata takarda ta musamman mai dauke da shafi 13 wadda Obasanjo ya fitar a yau din nan (Talata), ya ce Shugaba Buhari bai yi abin da ake zata zai yi ba, don haka yake bashi shawara da kada ya tsaya takara domin ya ci gaba da rike mutuncinsa, kuma ya koma layin tsofaffin shugabanniwadanda za su rika bayar da shawara domin ciyar da kasar gaba.
Idan ba a manta, Obasanjo ya taba yin wata wasika a wancan lokacin zaben inda ya umarci tsohon shugaban kasa Gudloock Jonathan da kada ya tsaya takara domin ya gaza.