Obasanjo ya goyi bayan Buhari

Tsohon Shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo, ya yi kira ga ’yan Najeriya su zabi dan takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC, Janar Muhammadu Buhari a zaben bana.Jaridar Financial Times da ake bugawa a birnin Landan ce ta ruwaito haka, a makon jiya a birnin Kano, Cif Obasanjo ya ce ba zai yi magana kan […]

Obasanjo ya goyi bayan Buhari
Obasanjo ya goyi bayan Buhari

Tsohon Shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo, ya yi kira ga ’yan Najeriya su zabi dan takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC, Janar Muhammadu Buhari a zaben bana.
Jaridar Financial Times da ake bugawa a birnin Landan ce ta ruwaito haka, a makon jiya a birnin Kano, Cif Obasanjo ya ce ba zai yi magana kan siyasa ba, sai bayan an kammala zaben bana, to amma sai ga shi ya bara a birnin Nairobi na kasar Kenya a ranar Litinin, lokacin kaddamar da littafinsa mai shafuka 1,500, inda a ciki ya yi mummunar suka ga Jonathan saboda rashin iya gudanar da mulki.
Wannan ne karo na farko da Obasanjo ya fito fili ya nuna goyon baya ga Janar Buhari.
A hirarsa da jaridar Financial Times bayan kaddamar da littafin, Cif Obasanjo ya yi watsi da masu sukan Buhari da cewa dan mulkin kama-karya nem inda ya ce: “Idan Buhari ya ci zabe zai gudanar da mulki na daban, ba irin wanda ya yi ba lokacin yana mulkin soji. Domin a lokacin mulkin soja shi ne Shugaban kasa kuma shi ne Shugaban Majalisa, ba irin yanzu ba. Kuma shi mutum ne mai hikima, yana da ilimi, yana da kwarewa. Don haka me ya sa ba zan goyi bayansa ba?”
Cif Obasanjo ya ce yana da yakinin Buhari zai iya magance cin hanci da rashawa, ya dawo da karfin gwiwa ga sojojin Najeriya da suke fuskantar barazana daga mayakan Boko Haram wadanda suka kwace wani bangare na kasar nan a yankin Arewa maso Gabas.
 “Batu ne na shugabanci – siyasa da aikin soja,” inji Obasanjo wanda yake magana kan matsalar da take fuskantar soja.
Ya kara da cewa, “Ina jin ya kamata ku tambayi (Jonathan) yaya aka yi ya bari (sojoji) suka samu kansu a wannan yanayi… abubuwa da dama suna tafiya ba daidai ba: daukar sojoji bai tafiya daidai; ba su horo bai tafiya daidai; an karya musu kwarin gwiwa; ba a karfafa musu gwiwa; ga muguwar almundahana; rashin kula da jin dadinsu ya tsananta.”
Sai ya gargadi Shugaba Goodluck Jonathan kan yiwuwar yin juyin mulki idan aka murguda hanyoyin gudanar da zaben bana, kuma ya soki Jonatha da kokarin zubar dab kimar sojojin Najeriya.
Ya kara da cewa yana fata Shugaba Jonathan ba so yake ya tarwatsa kasar nan ba game da batun dage zabe.