Obasanjo ya kafa gonar mangoro a Benuwai
Tsohon Shugaban Kasa Cif Olusegun Obasanjo ya kafa wata babbar gonar itatuwan mangoro mai fadin eka dubu 20 a kauyen Howe da ke Karamar Hukumar Gwer ta Gabas a Jihar Benuwai. Da yake zantawa da ’yan jarida lokacin da ya ziyarci gonar, Cif Olusegun Obasanjo ya ce a wannan gona akwai ma’aikata 40 daga cikin […]
Tsohon Shugaban Kasa Cif Olusegun Obasanjo ya kafa wata babbar gonar itatuwan mangoro mai fadin eka dubu 20 a kauyen Howe da ke Karamar Hukumar Gwer ta Gabas a Jihar Benuwai.
Da yake zantawa da ’yan jarida lokacin da ya ziyarci gonar, Cif Olusegun Obasanjo ya ce a wannan gona akwai ma’aikata 40 daga cikin ma’aikata 1,000 da za a dauka aiki.
Ya ce nan da shekara hudu masu zuwa za a fara dibar ’ya’yan mangwaron da aka shuka a gonar.
Ya ce gonar za ta taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin jihar a fannoni da dama.
Tsohon Shugaban Kasar ya ce hanyar kadai da za a iya rike Najeriya a matsayin kasa, ita ce a sanya jari a harkokin masana’antun sarrafa kayayyakin amfanin gona da ake nomawa a kasar nan.
Ya ce matukar ana son a bunkasa tattalin arzikin Najeriya, dole a rungumi harkokin noma.
“A kowace jiha a Najeriya, muna cin abinci. Man fetur abu ne da zai iya karewa, amma kasar da muke noma abincin da muke ci, ba za ta taba karewa ba. Don haka mu rungumi aikin noma a kasar nan, domin shi ne mafita,” inji Obasanjo.
A nasa bayanin Gwamnan Jihar Benuwai Samuel Ortom wanda ke tare da tsohon Shugaban Kasar, ya bayyana irin gudunmawar da Cif Obasanjo ya bayar wajen bunkasa noma a Najeriya lokacin da yake mulkin soja, ta hanyar kirkiro shirin ciyar da kasa da abinci.
Gwamnan ya yi kira ga masu zuba jari kan harkokin noma su yi kokarin zuwa jihar, saboda dimbin albarkar kasa da jihar take da shi.
Ya ce a shirye gwamnatinsa take ta tallafa wa masu zuba jari ta hanyoyi da dama.