Obasanjo ya kara caccakar Shugaba Jonathan

Tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya ce mulkin dimokuradiyya a Najeriya yana cikin hadari a sakamakon sakacin gwamnati mai ci a yanzu.Obasanjo ya fadi haka ne a Abuja, yayin da ake bikin kaddamar da littafi kan tsohon Shugaban Hukumar Yaki da Almundahana (ICPC), Mustapha Akanbi. A matsayinsa na shugaban taron, Obasanjo ya ce ya dace […]

Obasanjo ya kara caccakar Shugaba Jonathan
Obasanjo ya kara caccakar Shugaba Jonathan

Tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya ce mulkin dimokuradiyya a Najeriya yana cikin hadari a sakamakon sakacin gwamnati mai ci a yanzu.
Obasanjo ya fadi haka ne a Abuja, yayin da ake bikin kaddamar da littafi kan tsohon Shugaban Hukumar Yaki da Almundahana (ICPC), Mustapha Akanbi. A matsayinsa na shugaban taron, Obasanjo ya ce ya dace Shugaba Jonathan ya daina karfafa wa masu cacar bakin kare gwamnatinsa gwiwa, domin hakan na iya haddasa tashe-tashen hankali a kasa.
Ya kuma zargin gwamnatin ta yanzu da cewa tana ta kokarin cin zarafi da kashe kokarin jam’iyyun adawa, wanda haka kamar kashe dimokuradiyya ne. “A matsayinka na Shugaban kasa, bai dace ka aikata ko daure wa mummunan aiki gindi ba. Ya kamata ka sani cewa akwai ranar da za ka yi bayanin abin da ka aikata a gaban Allah. Za ka iya yin rufa-rufa a nan duniya, amma a gaban Allah, ba za ka iya rufe komai ba.” Inji tsohon shugaban kasar.
Obasanjo ya nuna bacin ransa sosai game da ta’addancin ’yan Boko Haram da yadda ake sace dukiyar gwamnati da yadda rashin aikin yi ya yi katutu da kuma yadda al’amuran tattalin arzikin kasa ya tabarbare. Kamar yadda ya ce, ba gaskiya ba ne da ake cewa wai ’yan Boko Haram suna aika-aikarsu ne da nufin dakile mulkin wani. Ya nuna takaicin yadda Shugaba Jonathan ya kwashe shekaru ba tare da ya magance wannnan matsala ta ’yan ta’adda ba.
Da yake bayani game da yadda sace-sacen dukiyar gwamnati ya zama ruwan dare a Najeriya, ya ce: “A yayin da kai (shugabanci) ya rube, gangar jiki ba ta da wani amfani.”
Game da tattalin arzikin kasa kuwa, ya ce zai ci gaba da tabarbarewa domin kuwa abin da masu rike da mulki suke fadi wa talakawa game da shi, cewa babau matsala ba gaskiya ba ne.
“Wannan gwamnatin ta gaza.” Inji Obasanjo, a yayin da aka tambaye shi ko me zai ce game da gwamnatin Jonathan. Ya kara da cewa ya kamata shi kansa a yaba masa, saboda ya taimaka an samu wani mutum daga tsirarun kabilu ya zama Shugaban kasar Najeriya. “Maimakon wasu da ke zargina don na taimaka Jonathan ya zama Shugaban kasa, kamata ya yi a yaba mani.” Inji shi.
A nata bangaren, fadar Shugaban kasa Jonathan ta mayar da martani ga Obasanjo, inda mai taimaka wa shugaban ta fuskar al’amuran jama’a, Doyin Okupe ya ce duk abin da tsohon shugaban kasar ya fada ba gaskiya ba ne. Ya ce abin da ya fada daidai yake da karkatar da ainahin gaskiya game da mulkin Shugaba Jonathan.

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi