…Obasanjo ya rike girmansa ya bar Jonathan ya fuskanci zabe – Mafindi

Mataimakin Daraktan Labarai na Kwamitin Kamfe na Shugaban kasa Goodluck Jonathan, Yarima Isa Mafindi, ya shawarci tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya kame bakinsa daga yawan sukar da yake yi ga Shugaba Jonathan.  Yarima Mafindi wanda ya bayyana haka a yayin da ya ke yiwa ’yan jarida bayani a farkon makon nan a kan zargin […]

…Obasanjo ya rike girmansa ya bar Jonathan ya fuskanci zabe – Mafindi
…Obasanjo ya rike girmansa ya bar Jonathan ya fuskanci zabe – Mafindi

Mataimakin Daraktan Labarai na Kwamitin Kamfe na Shugaban kasa Goodluck Jonathan, Yarima Isa Mafindi, ya shawarci tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya kame bakinsa daga yawan sukar da yake yi ga Shugaba Jonathan. 

Yarima Mafindi wanda ya bayyana haka a yayin da ya ke yiwa ’yan jarida bayani a farkon makon nan a kan zargin da Cif Obasanjo ya yi ga Jonathan na niyyar kin yin zabe tare da neman karin wa’adin gwamnati, inda ya kamanta shi da tsohon Shugaban kasar Kwaddibuwa Laurent Gbagbo, ya shawarci tsohon Shugaban kasar ya bar Jonathan ya fuskanci zabe maimakon ya rika tsangwamarsa.
Ya ce “Janar Obasanjo na da hanyoyi da dama da zai kai ga Shugaban kasa ya gaya masa duk abin da yake ji, maimakon ya rika sukansa ta kafafen watsa labarai. Na daya shi mamba ne a Majalisar kasa, na biyu bai da shamaki idan yana son ya ga Shugaba Jonathan a duk lokacin da yake so saboda darajarsa. Tsarin da yake bi na bayanai masu nauyi ta kafofin labarai, na iya tada zaune-tsaye.”
Ya kara da cewa, “Misali dauki maganar da ya yi cewa Shugaban kasa da Jam’iyyar PDP sun shirya yadda za su aiwatar da magudin zabe, ashe ke nan idan aka yi zabe Jam’iyyar PDP ta ci, an yi magudin zabe ke nan. Wannan karin lokaci da a ka yi, hurumi ne na Hukumar Zabe ta kasa (INEC) kuma bai saba tsarin dokokin zabe ba, shi kansa Janar Buhari ya yarda da hakan, mu ma a jam’iyyarmu ta PDP mun yarda da haka, me ya sa zai ce abin bai yi daidai ba? A ina ne ya ji cewa Shugaban kasa na shirin kafa gwamnatin rikon kwariya?”
Shi ma a jawabinsa Daraktan Labarai na Kamfe din Jonathan, Femi Fani-Kayode cewa ya yi, kwamitinsu da PDP na daukar tsohon Shugaban kasar da kima da kuma girmamawa, sai dai salon suka babu kakkautawa da yake yi ga Shugaba Jonathan a yanzu, ya sa dole su sake lale.