Obasanjo ya rude, cewar fadar shugaban Najeriya

Fadar shugaban kasar Najeriya ta bayyana cewa, kalaman tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo alama ce ta rudewa. A wani rahoto da mai taimaka wa Obasanjo a harkar watsa labarai Kehinde Akinyemi ya fitar da ke cewa, wanda bai san ciwon kansa  bane kawai zai ci gaba da goyon bayan wannan mulkin da ake yi a […]

Obasanjo ya rude, cewar fadar shugaban Najeriya

Fadar shugaban kasar Najeriya ta bayyana cewa, kalaman tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo alama ce ta rudewa.

A wani rahoto da mai taimaka wa Obasanjo a harkar watsa labarai Kehinde Akinyemi ya fitar da ke cewa, wanda bai san ciwon kansa  bane kawai zai ci gaba da goyon bayan wannan mulkin da ake yi a Najeriya.

Obasanjo ya ce, wadanda ba su dace ba ne ke jagorancin Najeriya don haka kasar ta lalace, sanadiyyar rashin samun shugabanni nagari wanda suke aiki karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari.