Obasanjo ya tsoma baki a kan jayayyar sarautar Ife

Tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya tsoma baki a kan jayayyar nada sabon Ooni na Ife da gidajen sarautu 4 na masarautar Ife ke cewa shi ne ya kamaci ya fito da sabon sarki.Obasanjo, wanda ya ziyarci fadar Ooni na Ife domin jajanta wa iyali da masu rike da sarautu game da rasuwar Oba Okunade […]

Obasanjo ya tsoma baki a kan jayayyar sarautar Ife
Obasanjo ya tsoma baki a kan jayayyar sarautar Ife

Tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya tsoma baki a kan jayayyar nada sabon Ooni na Ife da gidajen sarautu 4 na masarautar Ife ke cewa shi ne ya kamaci ya fito da sabon sarki.
Obasanjo, wanda ya ziyarci fadar Ooni na Ife domin jajanta wa iyali da masu rike da sarautu game da rasuwar Oba Okunade Sijuwade, ya nemi masu zaben sabon sarki a masarautar Ife su tabbatar sun yi aiki da tsare-tsaren da ake bi wajen zaben sabon sarki, domin guje wa aukuwar hargitsi. Ya ce: “Akwai bukatar masu zaben sabon Ooni na Ife su sanya tsoron Allah wajen zabo mutumin da ya cancanta, mai tsoron Allah da zai maye gurbin Ooni na Ife marigayi Oba Okunade Sijuwade.”
Obalufe na Iremo, Oba Solomon Omisakin, wanda ya karbi bakuncin tsohon Shugaban kuma ya yi magana a madadin zuriyar marigayin da manyan  hakiman masarautar, ya tabbatar wa tsohon Shugaban cewa: “Za mu tabbatar da cewa mun bi tsare-tsaren da muka yi gadonsu kaka da kakanni wajen zaben sabon Ooni na Ife. Duk mutumin da muka zaba a wannan kujera zai zama karbabbe ne ga al’ummar wannan masarauta ba tare da wani hargitsi ya auku ba.”
Kafin Obasanjo ya kai wannan ziyara ta ranar Juma’a, sai da zuriYar gidan sarauta ta Osinkola suka bayyana matsayinsu a ranar Alhamis a kan batun tsarin karba-karba a tsakanin gidajen sarautu hudu na masarautar Ife inda suka ce babu ruwansu da wannan tsari, domin babu dokar da ta kafa shi. Mai magana da yawun gidan sarautar Osinkola, Yarima Olakunle Aderemi, ya shaida wa ’yan jarida a Osogbo cewa, shekaru da yawa da suka shude aka daina yin aiki da tsarin karba-karba wajen zaben sabon Ooni na masarautar  Ife, saboda haka kofa bude take ga dukkan mai sha’awar hayewa bisa wannan karaga daga gidajen sarautu hudu.
Bayanin da wakilinmu ya jiyo daga wata majiya a ofishin Gwamnan Jihar Osun, Ogbeni Rauf Aregbesola, ya nuna cewa, yanzu haka Ma’aikatar kananan Hukumomi da Harkokin Masarautun Gargajiya ta Jihar ta aike da rubutacciyar takarda da ta shafi tsare-tsaren nada sabon Ooni ga Gwamnan, domin fara tattaunawa a kan wannan matsala.
“Dokar nada sabon sarki a Jihar Osun ta tsara yadda gwamnati za ta fara aikin cike gurbi ta hanyar aikewa da wasiku zuwa ga gidajen sarautu 4 da su fito da ’yan takara masu sha’awar hawan karaga a cikin kwana 14 da mutuwar sarki,” inji majiyar, wacce ta tabbatar da cewa yanzu haka ana tattaunawa a kan batun, musamman da yake Gwamnan Jihar, mutum ne mai girmama al’adu da suka shafi sarautun gargajiya.