Obasanjo ya yi laifuka 126 da ya kamata a tsige shi daga Shugaban Kasa – Abdulkarin Dayyabu

Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya yi laifuffuka 126 da kowanne da suka isa a tsige shi a lokacin da yake mulki, don haka bai cancanci ya rika caccakar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ba. Tsohon Shugaban Jam’iyyar AD ta Kasa kuma jagoran Kungiyar Forward for Buhari Alhaji Abdulkarim Dayyabu ne ya bayyana haka  lokacin da […]

Obasanjo ya yi laifuka 126 da ya kamata a tsige shi daga Shugaban Kasa – Abdulkarin Dayyabu

Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya yi laifuffuka 126 da kowanne da suka isa a tsige shi a lokacin da yake mulki, don haka bai cancanci ya rika caccakar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ba.

Tsohon Shugaban Jam’iyyar AD ta Kasa kuma jagoran Kungiyar Forward for Buhari Alhaji Abdulkarim Dayyabu ne ya bayyana haka  lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja.

Ya ce Jam’iyyar PDP na kukan za a murde zaben ne kawai saboda ta ga cewa za ta fadi.

Abulkarim Daiyabu ya ce ya kamata ’yan Najeriya su tambayi Obasanjo ya yi bayanin yadda ya yi da kudaden da Najeriya ta samu lokacin yana Shugaban Kasa ciki har da Dala biliyan 16 da aka batar wajen gyara wutar lantarki. “Abin da Najeriya ta samu tsakanin 1999 zuwa 2015 ya fi abin da kasar ta samu tun daga 1914 da aka hada kasar nan zuwa 1999. Ina kudin suke? Mun san muna da Dala miliyan 16 a hannunsa na wutar lantarki.Kuma za ku iya tuna cewa lokacin da yake Shugaban Kasa ya yi laifuffuka 126 da suka cancanci a tsige shi, amma maimakon a tsige shi, ya bige da tsige shugabannin majalisa. Da yardar Allah komai zai dawo daidai, kuma za a yi waiwaye tare da magance duk abubuwan nan,” inji shi.

Ya ce kungiyarsu a shirye take wajen taimaka wa ci gaban da ake samu yanzu haka wajen habaka tattalin arzikin kasar nan da kuma gyara siyasarta, inda ya kara da cewa sun taru ne domin tattara masu kishin kasar nan wajen ciyar da kasar gaba.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa