Obasanjo ya yi magana gwamnati ma ta yi, saura `yan kasa

daya da daya yau a kasar nan, ba mutum daya tilo da ya zama kanwa uwar gami cikin harkokin tafiyar da gudanarwar mulkin kasar nan na tsawon shekaru aru-aru, irin tsohon shugaban kasar nan a mulkin soja da farar hula Cif Olusegun Obasanjo. Tarihi ya tabbatar da cewa tunda Cif Obsanjo ya bar mulki a […]

Obasanjo ya yi magana gwamnati ma ta yi, saura `yan kasa

daya da daya yau a kasar nan, ba mutum daya tilo da ya zama kanwa uwar gami cikin harkokin tafiyar da gudanarwar mulkin kasar nan na tsawon shekaru aru-aru, irin tsohon shugaban kasar nan a mulkin soja da farar hula Cif Olusegun Obasanjo. Tarihi ya tabbatar da cewa tunda Cif Obsanjo ya bar mulki a gwamnatin mulkin soja a shekarar 1979, ya kuma mika wa zababben shugaban farar hula Alhaji Shehu Shagari na jam`iyyar NPN, mulki a wancan lokaci, ba a taba yin wata gwamnati walau ta farar hula ko ta soja da ya sakar wa mara ta tafiyar da mulkin kasar nan kamar yadda ya kamata, face gwamnatinsa ta farar hula da ya jagoranta tsakanin shekarun 1999 zuwa 2007.

Bari in fara da shekarar 1984, da sojoji suka hambarar da gwamanatin farar hula ta Alhaji Shehu Shagari, Janar Muhammadu Buhari ya zo kan karagar mulki, `yan kasa sun ta tsammanin Obasanjo, zai yi gum da bakinsa ya zama dattijon kasa mai ba da shawara tagari, amma haka ya ci gaba da caccakar gwamnatin mulkin sojan ta Buhari, bisa ga ganin wallanta na rashin iya tafiyar da mulki, musamman kin fito da jadawalin ranar da za ta mayar da mulkin hannun farar hula. Har ya zuwa ranar 27 ga watan Augustan 1985 da sojoji suka yi wa Janar Buhari juyin mulki, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya hau kan karagar mulki. 

Gwamnatin mulkin soja ta Janar Babangida an yi ta tsanmanin kasancewar ta murucin kan dutse da ake cewa bai fito ba sai da ya shirya, an yi ta tsammanin Cif Obasanjon zai kauda kai a kanta tare da sakar mata mara ta tafiyar da mulki yadda take bukata bisa zargin kamar ‘yar lelansa ne a cikinta, amma da tafiya ta yi nisa sai ga shi Cif Obasanjo ya na bayyana gwamnatin Babangidan da cewa “idan ta ce da kai barka da asuba, to karka amsa, sai ka daga labulan tagarka ka ga idan rana ta fito,” bisa ga wai tsabagen yaudara irin ta gwamnatin Babangida. 

Haka ya ci gaba a kan gwamnatin tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha, wanda ya yi wa shugaban gwamnatin rikon kwarya Cif Enest Shonekan, wanda bayan matsin lambar da Babangida ya fuskantar ala tilas ya ba shi mulki a ranar 27 ga watan Augustan 1993. Tsohon shugaban kasa Janaral Abacha ne kawai ya yi ta maza ya kame Cif Obasanjo ya kuma daure shi rai da rai bisa ga zargin ya yi yunkurin juyin mulki ga gwamnatinsa, haka kuwa ba ya rasa nasabar da irin ci gaba da sukar gwamnatin Abacha, kamar yadda ya yi ta yi ga wadanda suka rigaye shi.

Bayan rasuwar Janar Abacha a cikin watan Yunin 1998, Janar Abdussalami Abubakar ya hau kan karagar mulki ne, gwamnatinsa ta yanke shawarar ba gudu ba ja da baya za ta mayar da mulki a hannun farar hula a ranar 29 ga watan Mayun 1999, (wato bayan shekara daya da hawansa mulki). Gwamnatin Abdussalami din da shawarar manyan tsofaffin hafsoshin soja irin su tsohon shugaban kasa Babangida da Janaral Yakubu danjuma da sauran masu fada a ji, suka sa aka yafe wa Cif Obasanjo, sannan kuma kai tsaye bayan sako shi suka sa shi cikin jam’iyyar PDP, tare da ba shi takarar neman shugabancin kasar nan a zaben shekarar 1999, inda kuma ya yi nasara. 

Haka Cif Obasanjo ya shafe shekaru takwas cur a zaman shi na shugaban kasar farar hula a wannan jamhuriya ta hudu da muke ciki yana ta kama karyarsa yadda ya ga dama, kai ka ce ba mulkin farar hula ake ba. A lokacinsa ne ya rinka yayin cire shugabannin jam’iyyarsu ta PDP ta kasa baki daya ba tare da wani zai fi ba irin su shugabanta na farko Cif Solomo Lar da Sanata Barnabas Gemade, tare da sauke Ministocin da zuciyarsa ta raya masa ya sauke kasancewar dama tun daga ranar da ya rantsar da su ya basu wata takarda da ta ke dauke da bayani zai iya sallamarsu koda yaushe ya ga dama. A lokacin nasa ne harkokin samar da wutar lantarki ga hanyoyin mota na kasar nan su ka tabarbare ta yadda duk da ya ke a lokacin ya kashe Dalar Amurka wuri na gugar wuri har $16biliyan kuma wutar ba ta gyaru ba, haka ma a fannin hanyoyi. 

Haka Obasanjo ya yi ta bidirinsa daga karshe kuma saboda jin dadin mulki ya nemi ya yi TAZARCE, amma Allah Ya karya shi. Ganin TAZARCEN ba ta samu ba, ta sanya Cif Obasanjo ya dauko tsohon gwamnan jihar Katsina marigayi Umaru Musa ‘Yar’aduwa da tsohon gwamnan jihar Bayelsa Dokta Goodluck Jonathan ya ba su takarar neman shugabancin kasar nan a zaman shugaba da mataimakinsa a zaben shekarar 2007 a inuwar jam’iyyarsu ta PDP. Duk da shugaba ‘Yar’aduwa ya yi ta laulayin rashin lafiya da irin kokarin ya kamanta gyaran kasa a cikin shekaru uku da ya yi Allah Ya dauki ransa a watan Aprilun 2010, Obasanjo sai da ya fara tsokanarsa a zaman gazawa cikin mulki. 

Bayan Dokta Jonathan, wadanda akasarin ‘yan kasa suka hakkake da cewa Cif Obasanjo ya dauke shi tamfar dansa ya kuma mara masa baya dari bisa dari ya ci zaben shekarar 2011, amma sai ga shi an gansu a rana har ta kai fagen da don Cif Obasanjo ya nuna ba ya tare da Jonathan a zaben 2015, ta kai ga sau biyu yana rubuta wa Shugaba Jonathan budaddiyar wasikar da yake tir da Allah wadai da salon mulkin shugaba Jonathan. karshe ma dai don Cif Obasanjo ya nuna sam-sam baya tare da Jonathan da gwamnatinsa, sai da ya tara taron shugabannin mazabarsa inda abainar duniya ya bayyana fucewarsa daga jam’iyyar PDP, karshe ma dai ya tabbatarwa da duniya da gaske ya ke ya kekketa katinsa na dan jam’iyyar PDP. 

Haka dai ya yi, aka ba shi dama ya dawo karkashin neman takarar shugabancin kasa na Muhammadu Buhari a sabuwar jam’iyyar APC, da wasu jam’iyyun hadaka irinsu ACN da ANPP da wani bangare na gwamnonin PDP biyar da bangaren APGA. Wanna hadaka da Cif Obasanjo ya shiga ba da sunan dan jam’iyyar APC ba, ita ta kai Shugaba Muhammadu Buhari ga nasarar lashe zaben shekarar 2015.

Mai karatu daga wannan tarihi na siyasar Cif Obasanjo cikin kusan shekaru arba’in dana dan iya kawo maka bai zama wani abin mamaki ba a yau don Cif Obasanjo ya aikawa shugaba Buhari budaddiyar wasika inda ya ke shawartarsa da kada ya kuskura ya ce zai sake neman takarar shugabancin kasar nan a badi bisa ga abin da ya yi zargin bai tabuka komai ba. A cikin wasikar Cif Obasanjo ya nemi ‘yan kasa da su zo su kafa hadakar da za ta ceci kasar nan. Zuwa yanzu jam’iyyar APC ta mayar da martani cikin lumana ga Obasanjo, tare da hankaltar da shi irin nasarorin da suka samu a kan manyan batutuwa uku da ta yi wa ‘yan kasa alkawari lokacin yakin neman zabe, wato yaki da cin hanci da rashawa da ‘yan ta’adda da kuma farfado da tattalin arzikin kasa kamar yadda Ministan Yada labarai Alhaji Lai Muhammed ya bayyana wa duniya. Saura da me yanzu? Ya ragewa ‘yan kasa musamman ma’abota hankali su duba tarihin rayuwar Obasanjo, sannan su yi wa kansu alkalanci akan ko Cif Obasanjo dattijon da za a rinka daukar maganarsa ne? Shi ma shugaba Buhari yana bukatar ya kara mike wa tsayin daka.