Obaseki ya cika alƙawarin ƙarin albashi a Edo

Ma’aikata sun fara karɓar N70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi a Edo.

Obaseki ya cika alƙawarin ƙarin albashi a Edo

Godwin Obaseki, Gwamnan Jihar Edo

Gwamna Jihar Edo, Godwin Obaseki wanda a yayin bikin Ranar Ma’aikata ta 2024 ya ƙara wa ma’aikata albashi mafi ƙaranci daga Naira 40,000 zuwa Naira 70,000, ya cika alƙawarin da ya yi don daƙile illolin da taɓarɓarewar tattalin arziki ke yi wa al’ummar jihar.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan Sadarwa da Wayar da Kan Jama’a na jihar, Chris Nehikhare ya fitar.

Kwamishinan ya ce biyan mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000 ga ma’aikata, ya ƙara nuna irin sadaukarwar da gwamnatin Gwamna Godwin Obaseki ke yi na kyautata jin daɗin ma’aikatan Edo.

Ya ce, “Gwamnatin jihar ta biya mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000 a watan Mayu, wanda hakan ke nuna yadda aka aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashin.

“Wannan cika alƙawarin da Gwamna Godwin Obaseki ya yi ne a farkon watan Mayu, a wani ɓangare na ƙoƙarin daƙile ƙuncin da al’umma ke fuskanta sakamakon cire tallafin mai da sauran matsalolin tattalin arziki.”

Kwamishinan ya buƙaci ma’aikatan jihar su jajirce wajen gudanar da ayyukansu, tare da bayar da gudunmawa yadda ta kamata domin saka wa gwamnatin jihar a kan na kyautata rayuwarsu.