Obudu: Gari mai itaciyar kuka da ta shekara 182

Bishiya ce mai cike da dimbin tarihi a garin

Obudu: Gari mai itaciyar kuka da ta shekara 182

Wata bishiyar kuka

Wata itaciyar kuka ta shafe sama da shekara 180 a garin Obudu da ke Jihar Kuros Riba.

Tarihin wannan itaciyar na da nasaba ne da yadda Hausawa suka fara zama a wurin kamar yadda Aminiya ta samu labari, inda aka ce Hausawa sun zauna a wurin sama da shekara 100 a kusa da wani rafi da suke kamun kifi da koma domin samun abin da za su rika cin abinci.

Bayanai sun ce wadancan Hausawan ne suka sanya wa rafin suna Rafin Raga kafin daga bisani a yi gada a wurin kamar yadda Aminiya ta samu labari.

Wannan wuri yana kan hanyar zuwa Ogoja, kuma har yanzu da sunan Rafin Raga ake kiran wurin.

Bayanai sun ce Hausawan sun shafe shekaru a wajen inda suka shuka itatuwa irin na Arewa kamar zogale da dalbejiya da kukar wadda ita ce ta fi dadewa.

Da Aminya ta ziyarci wurin, a karkashin itaciya ta tarar akwai kwarin kwarkwasa, wadanda wasu ke ganin wannan ma wata alama ce da ke nuna lallai Hausawa sun zauna wurin da ake kira Obudu tsohon gari, inda nan ne ake zaune a yankin kafin daga bisani a koma Sabon Garin Obudu .

Hausawan dai akasari Gobirawa ne masu su ko farauta da ake zaton sun fito ne daga tsohuwar Jihar Sakkwato don su da farautar namun daji da suka hada da giwaye da suka addabi manoman yankin Obudu.

An ce basaraken garin na wancan lokaci ne ya ba su wurin suka zauna.

Alhaji kasimu Ali Haruna, Sarkin Hausawan Obudu ya yi wa Aminiya karin bayani game da wannan kuka da kuma Gobirawan da suka zauna a tsohon garin sama da shekara 150.

“Wannan wuri da ka gani nan ne ainihin inda Hausawa suka fara zama sama da shekara 150 kafin a koma Obudu Sabon Gari.

Ya ci gaba da cewa, “Ita kuma wannan itaciyar kuka da ka gani shekarunta za su kai 182 ka ga ko kawa cikin garin Obudu Sabon Gari ya fi shekara 60 tunda a nan aka haifi iyayenm, su kuma suka haife mu,” inji Sarkin.

Wakilinmu ya zagaya kasuwa ta farko da ’yan Arewa suka kafa sai dai ya tarar yanzu wurin ya zama mazaunin gineginen gwamnati.