Odegbami zai yi takarar shugabancin Hukumar FIFA

Tsohon kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Green Eagles Segun Odegbami ya bayyana aniyarsa na tsayawa takarar shugabancin hukumar FIFA wanda za a yi a ranar 26 ga  Fabrairun shekarar 2016 idan Allah Ya kaimu.A wata takarda da ya fitar ta hannun shugaban kwamitin yi masa kamfe na neman shugabancin hukumar Dokta Ade Adegbo, Odegbami […]

Odegbami zai yi takarar shugabancin Hukumar FIFA
Odegbami zai yi takarar shugabancin Hukumar FIFA

Tsohon kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Green Eagles Segun Odegbami ya bayyana aniyarsa na tsayawa takarar shugabancin hukumar FIFA wanda za a yi a ranar 26 ga  Fabrairun shekarar 2016 idan Allah Ya kaimu.
A wata takarda da ya fitar ta hannun shugaban kwamitin yi masa kamfe na neman shugabancin hukumar Dokta Ade Adegbo, Odegbami ya yanke shawarar yin takarar ce don ya kawo karshen  matsalar cin hanci da rashawa da ta dabaibaye hukumar.
Kamar yadda Odegbami ya nuna, abin kunyar da ya faru na dambarwar cin hanci da rashawa shi ne irinsa na farko a tarihin hukumar a tsawon shekara 111 da kafuwarta.
“Yakamata na tsaya takarar ce don na kawo sauyi mai ma’ana a matsayina na matashi mai kananan shekaru don na lura Sepp Blatter da mukarrabansa sun gaza wajen gudanar da shugabanci nagari a hukumar ta FIFA”.