Ododo ya rantsar da sabbin shugabannin ƙananan hukumomi a Kogi

Gwamnan ya buƙaci sabbin shugabannin su mayar da hankali wajen yi wa al’umma hidima.

Ododo ya rantsar da sabbin shugabannin ƙananan hukumomi a Kogi

Gwamnan Jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo, ya rantsar da sabbin zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomi 21 tare da mataimakansu.

An gudanar da bikin rantsuwar ne a dakin taro na Banquet Hall da ke Gidan Gwamnati a Lokoja, a ranar Litinin.

Gwamna Ododo ya ƙarfafi gwiwar sabbin shugabannin su ci gaba da gudanar da ayyukan da za su inganta rayuwar al’umma a jihar.

Haka kuma, ya tunatar da su muhimmancin tsaron rayuka da dukiyoyin mutanen yankunansu, da kuma taimaka wa shirye-shiryen gwamnati a ɓangarorin lafiya da noma da walwalar al’umma.

Gwamnan ya kuma buƙaci sabbin shugabannin su tabbatar da sun haɗa kai da al’umma a dukkanin ayyukansu.

“Dole ne ƙananan hukumomi su kasance kusa da mutane tare da tabbatar da cewa al’umma suna ganin tasirin shugabancinsu.

“Dole ne ku kasance masu gaskiya da rikon amana wajen tafiyar da ayyukan ƙananan hukumomi.

“Zaɓar ku dama ce ta nuna muhimmancin ’yancin ƙananan hukumomi ta hanyar ba da fifiko ga abubuwan da za su inganta rayuwar mutane a matakin ƙasa,” in ji Gwamna Ododo.

Shugaban ƙaramar hukumar Yagba ta Yamma, Tosin Olokun, wanda ya yi magana a madadin sauran shugabannin guda 20, ya tabbatar wa gwamnan cewar za su yi aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin jihar.

Haka kuma, ya yi alƙawarin haɗa kan al’umma, duk da bambancin siyasa, tare da mayar da hankali kan ci gaba kamar yadda gwamnatin jihar ke so.

Yadda aka yi sulhu da ’yan bindigar Kaduna

‘Da kuɗin yankan farce na je Hajji’

Zambar Intanet: EFCC ta kama ’yan China 4 da wasu 101 a Abuja

Gwamnan Akwa Ibom ya kori duk Kwamishinoninsa