Ofishin jakadancin Amurka na neman haxin gwiwa da Jami’ar NOUN

Ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja zai haxa gwiwa da jami’ar NOUN domin qara faxaxa harkokin jami’ar. Mataimakin shugaban vangaren tattalin arziki na ofishin jakadancin Mista Joel A. Koop ne ya sanar da hakan a lokacin da ya kawo ziyara ofishin shugaban jami’ar farfesa Abdalla Uba Adamu a hedkwatar jami’ar a Abuja. Mista Koop wanda […]

Ofishin jakadancin Amurka na neman haxin gwiwa da Jami’ar NOUN

Ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja zai haxa gwiwa da jami’ar NOUN domin qara faxaxa harkokin jami’ar.

Mataimakin shugaban vangaren tattalin arziki na ofishin jakadancin Mista Joel A. Koop ne ya sanar da hakan a lokacin da ya kawo ziyara ofishin shugaban jami’ar farfesa Abdalla Uba Adamu a hedkwatar jami’ar a Abuja.

Mista Koop wanda ya samu rakiyar Mis Sarah Young ya ce a matsayinsa na xaya daga cikin ma’aikatan vangaren tattalin arzikin na ofishin jakadancin, suna so su haxa gwiwa ne da jami’ar ta NOUN domin gyara jadawalin karatun vangaren tattalin arziki da kuma samar da hanyoyin zuba jari.

“Muna tunanin zai taimaka sosai idan muka haxa gwiwa da jami’a a Abuja, wanda hakan ne ya sa muka zo jami’ar NOUN da buqatar mu.

“Mun amince da abun da ku ke yi a wannan jami’ar wajen tarbiyantar da manyan gobe na qasar nan. Muna so xalibanku so san sauran vangarorin ofishin jakadancin,” inji Koop.

Mista Koop ya qara da cewa a matsayinsu na ofishin jakadanci, ba wai suna buqatar magana tsakanin gwamnati da gwamnati ba ne kawai, har ma da tsakanin mutane da mutane, da kuma ofishin jakadanci da mutanen gari.

A lokacin da shugaban jami’ar ke mayar da jawabi, ya yi maraba da haxin gwiwar da ofishin jakadancin sannan ya buqaci ofishin jakadancin da ya buxe lungun Amurka a sassan jami’ar da ke faxin qasar nan baki xaya domin sauqaqe hanyar isar da saqon da ofishin jakadancin ke son isar wa.

Ya ce, a matsayin jami’a na ma fi girma a yankin Afirka ta yamma, haxin gwiwa da sashen tattalin arziki na ofishin jakadancin ba qaramin abun maraba ba ne.

Farfesa Adamu ya shaida wa baqin cewa tsare-tsaren jami’ar an shirya su ta yadda za su magance matsalar ta’addanci musamman a yankin Arewa maso Gabas inda rikicin ya fi qamari.

“Tsare-tsaren mu suna taimakawa wajen magance matsalar ta’addanci. Duk da cewa akwai matsalar talauci, amma mun yi imanin cewa idan mutane suka samu ilimi, za su yi abun da ya kamata. Za mu iya yaqar ta’addanci da ilimi.

“Mun bayar da dama ga waxanda aka watsar da su kuma aka ware su su yi karatu, da waxanda suka cire tsammani, da ‘yan fursuna da dai sauransu, yanzu burinmu shi ne mu koma vangaren matan yankin Arewa maso gabas domin suma mu ga abun da ya kamata,” inji shi.

Maqasudin buxe jami’ar NOUN, a cewarsa shi ne a samar wa mutane damar yin karatu alhali suna ci gaba da aikin su, sannan kuma tsarin jadawalin jami’ar ba wai zai qarfafa ilimin xaliban ba ne kawai, zai taimaka musu wajen nuna qwarewa a tsakanin sa’anni a wannan lokaci da tattalin arziki ke canjawa cikin sauri.