Ogun ta sa Hausa cikin harsunan faɗakarwa kan cutar kwalara

Kwamishinan ya yi gargaɗin cewa jihar ta samu rahoton ɓullar cutar fiye da ƙima.

Ogun ta sa Hausa cikin harsunan faɗakarwa kan cutar kwalara

Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Ogun ta sanya Hausa a cikin jerin harsunan da za ta yi amfani da su wajen faɗakarwa game da matakan da suka kamata jama’a su riƙa ɗauka don kauce wa kamuwa da cutar kwalara a jihar.

Tuni ma’aikatar ta shirya sanarwar ta musamman a cikin harsunan Yarbanci da Ingilishi da kuma Hausa, kuma jihar ta ce ta sanya harshen Hausa ne duba da tarin al’ummar Arewa da ke zaune a jihar, inda ake sanya faɗakarwar a gidan rediyo da talabijin na gwamnatin jihar.

A cikin sanarwar ana yin shela ce kan cutar kwalara inda ake bayyana hanyoyin da take yaɗuwa da hanyoyin riga¬kafinta. Sanarwar na cewa: “Kwalara cuta ce dake murɗe ciki wacce ake kamuwa da ita ta hanyar amfani da gurbataccen ruwa ko shiga bayan gida mara tsabta.

“A lokacin damina akwai yiwuwar ɓullar cutar kwalara saboda fashewar shadda ko ambaliyar ruwa, inda ake samun gurɓataccen ruwa da ka iya shiga ɗakin girki ko wasu muhimman wurare ya gurɓata su.

“Don haka wajibi ne mu tabbatar mun tsaftace ɗakin girki da ban-ɗaki tare da yawaita wanke hannu da kayan marmari kafin mu ci.

“Sannan mu guji shan gurɓataccen ruwa da ruwan da ya canja launi ko yake wari ko kuma ɗanɗano.

“Abu ne mai muhimmanci a tafasa ruwan sha tare da adana shi a mazubi mai kyau.

“Bugu da ƙari idan wani na kusa da kai ya kamu da amai da gudawa, wajibi ne a kai shi cibiyar lafiya mafi kusa don a ba shi kulawa.

“Don ƙarin bayani sai a kira wannan lamba: 07034214893.

“Wannan saƙon ya zo maku ne daga ma’aikatar lafiya ta jihar Ogun,” in ji sanarwar.

A ranar Litinin da ta gabata ce kuma Gwamnatin Jihar Ogun ta tabbatar da ɓullar cutar kwalara a  ƙananan hukumomi bakwai na jihar, inda mutum ɗaya ya rasu a Ƙaramar Hukumar Ijebu ta Arewa a Ogun ta Gabas.

Kwamishinar Lafiya ta Jihar, Dokta Tomi Coker ce ta bayyana haka yayin ganawa da manema labarai a Cibiyar ’Yan Jarida ta Olusegun Osoba da ke babban birnin jihar.

Ta ce an fara aikin sa ido da bayar da agajin gaggawa a dukkan ƙananan hukumomi 20 na jihar.

Ta ce ƙananan hukumomin Abeokuta ta Kudu da Abeokuta ta Arewa da Obafemi/Owode da Ijebu ta Arewa da Ado da Odo/ Ota ne wuraren da cutar ta fi ƙamari.

Sai ta bai wa jama’a tabbacin shirin gwamnatin jihar na ci gaba da tunkarar cutar, inda ta buƙaci mazauna yankin su kiyaye tsaftar jiki da muhalli domin dakile yaɗuwar cutar.

“A karin farko mun samu sanarwa a ranar 12 ga watan Yuni, 2024, game da samun mutum 2 da cutar, an yi amfani da na’urar gano cutar kuma an ba su kulawa a asibitin jiha da ke Ota,” in ji ta.

Ta ce mutum biyu na farkon sun je Jihar Legas sa’o’i 24 kafin cutar ta bayyana a jikinsu, bayan sun dawo, “Zuwa yau 24 ga watan Yuni, 2024, Jihar Ogun ta samu mutum 25 da ake zargin sun kamu da cutar kwalara a ƙananan hukumomi 7, wato Adoodo/Ota, Remo ta Arewa,

Odeda, Sagamu, Ijebu ta Arewa, Ewekoro da Obafemi Owode, kuma abin takaici mutum ɗaya ya rasu,” in ji ta.

Ta ce, tun kafin ɓarkewar cutar, an samar da ingantaccen tsarin sa ido a dukkan ƙananan hukumomi 20 na jihar.

Ta ƙara da cewa sashin kula da cututtuka na jihar yana cikin shirin ko-ta-kwana, kuma dukkan jami’an sa-ido kan cututtuka da faɗakarwa na ƙananan hukumomi suna aikin sa ido a ƙananan hukumomin jihar 20 .

A Jihar Legas kuwa, Ma’aikatar Lafiya ta Jihar ta sanar da mutuwar mutum 29 da kuma kamuwar mutum 579 da cutar bayan ɓarkewar cutar kwalara mako biyu da suka gabata a jihar.

Da yake zantawa da manema labarai a ranar Litinin, Kwamishinan Lafiya na Jihar, Farfesa Akin Abayomi, ya ce adadin mace-macen ya faru ne saboda an kai marasa lafiya a zuwa asibiti a makare da kuma waɗanda aka kai su a mace.

Ya ce ba a samu labarin kamuwa da cutar a makarantu a jihar ba.

“A mako biyu da suka gabata, mun samu rahoton mutuwar mutum 29 da kuma mutum 579 da ake zargin sun kamu da cutar kwalarar.

“Mutuwar mutum 29 ta faru ne sakamakon kai marasa lafiya a makare waɗanda ba za mu iya farfaɗo da su ba,” in ji shi.

A ranar 11 ga Yuni, 2022, a cikin wata sanarwa, Kwamishinan ya yi gargaɗin cewa jihar ta samu rahoton ɓullar cutar fiye da ƙima.

Farfesa Abayomi ya ce an samu ɓullar cutar ce mai tsanani a al’ummomin da ke kewayen Eti-Osa da Legas Island da Ikorodu da Ƙaramar Hukumar Kosofe a jihar.