Ohinoyi: Mace ta fito takarar kujerar Sarkin Ebira cikin maza 70

Mutum 71 ciki har da mace ne suke neman zama babban basaraken kasar Ebira (Ohinoyi)

Ohinoyi: Mace ta fito takarar kujerar Sarkin Ebira cikin maza 70

Mace daya maza 70 ne suke neman zama babban basaraken kasar Ebira (Ohinoyi) bayan rasuwar Mai Martaba Ado Ibrahim, wanda ya rasu ranar 29 ga Oktobar bana.

Sakatare Majalisar Masarautar Ebira, Alhaji Yunusa Sule, ya sanar cewa Farfesa Angela Oregwu-Okatahi, na daga cikin mutum 71 da suka yanki takardar tsayawa takarar ta zama Ohinonyi

Amma ya bayyana cewa, “Duk da cewa mutane 71 ne, amma daya daga cikinsu mace ce, wato Farfesa Angela Oregwu-Okatahi, kuma bisa al’adarmu ba ta cancanci hawa wannan gadon sarauta ba.”

Don haka, ya ce an soke takararta, yanzu “mutum 70 suke takarar daga yankuna hudu — Okewe, Ohema, Erika, Aganiye and Adavi ”.

Amma ya ce babu wanda ya fito takarar daga yankin Adavi ba, kasancewar marigayi Ohinoyi dan asalin yankin.

Masu neman sarautar Ohinoyin sun hada da tsohon mataikin gwamnan jihar, Philip Salawu; tsohon akawun Majalisar Dokoki ta Kasa, Ataba Sani Omolori (Ciroma of Ebiraland); Birgediya Yusuf Abubakar Amuda (murabus); da kuma Ohi na Okengwe, Mai Martaba Tijani Muhammed Anaje da sauransau.

Karamar Hukumar Okene ce a kan gaba wajen yawan ’yan takara da mutum 39, sai karamar hukumar Okehi mai 20, karamar hukumar Ajaokuta 7, sannan 5 daga Adavi .

Ranar Liiin 11 ga wannan waan na Disamba ne Gwamnain Kogi da sanar da fara aikin zabar magajin Ohinoyi Ado Ibrahim , har ta kafa kwamitin tantancewa da kuma zaben magajin nasa.

Tinubu ya dawo Abuja bayan halartar taro a Saudiyya

Zaɓen Ondo: Atiku ya gargaɗi INEC kan tafka maguɗin zaɓe

Sojoji sun tafka ƙazamin artabu da Bello Turji a Sakkwato 

Mutum 10 sun rasu a hatsarin mota a Jigawa