Ohinoyi: Sarkin Kasar Ebira ya rasu

Ya koma ga Mahaliccinsa yana da shekaru 94 a duniya, kuma bayan shekaru 25 a kan karagar mulkin Masarautar Ebira

Ohinoyi: Sarkin Kasar Ebira ya rasu

Allah Ya yi Sarkin Kasar Ebira, Ohinoyi Abdul Rahman Ado Ibrahim (CON) rasuwa.

Mai Martaba Abdul Rahman Ado Ibrahim, ya rasu ne a fadarsa da ke garin Okene a Jihar Kogi kafin wayewar garin Lahadi.

Ya koma ga Mahaliccinsa ne yana da shekaru 94 a duniya, kuma bayan shekaru 25 a karagar mulkin Masarautar Kasar Ebira da ke Jihar Kogi.

Ya hau mulki ne a shekarar 1997 bayan rasuwar Ohinoyi Sanni Omolori.

Tags