OIC ta ce Boko Haram ba Musulunci ba ne

kungiyar Hadin kan kasashen Musulmi (OIC) ta ce ayyukan kungiyar Boko Haram ba Musulunci ba ne, inda ta bayyana ’yan kungiyar Boko Haram a matsayin gungun ’yan ta’adda wadanda ta ce bai kamata a rika danganta su da addinin Musulunci ba.Babban Sakataren kungiyar Iyad Ameen Madani ne ya bayyana haka bayan ya jagoranci wakilan kungiyar […]

OIC ta ce Boko Haram ba Musulunci ba ne
OIC ta ce Boko Haram ba Musulunci ba ne

kungiyar Hadin kan kasashen Musulmi (OIC) ta ce ayyukan kungiyar Boko Haram ba Musulunci ba ne, inda ta bayyana ’yan kungiyar Boko Haram a matsayin gungun ’yan ta’adda wadanda ta ce bai kamata a rika danganta su da addinin Musulunci ba.
Babban Sakataren kungiyar Iyad Ameen Madani ne ya bayyana haka bayan ya jagoranci wakilan kungiyar wajen ganawa da Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan a ranar Litinin. Ya ce ayyukan Boko Haram sun saba wa Musulunci kuma suna cutar da Najeriya.
Iyad Madani ya kuma ce kasashe 57 mambobin kungiyar za su ci gaba da taimaka wa Najeriya a fafutikar da take yi na kawo karshen hare-haren ta’addanci a kasar.
Kafin ganawar, wakilan tawagar kungiyar sun gana da Ministan Harkokin Wajen Najeriya Ambasada Aminu Wali.
Kuma bayan ganawarsu da Shugaba Jonahan Iyad Madani ya ce sun je fadar Shugaban kasa ne domin sanin manufar Jonathan game da OIC da kuma bayyana goyon bayanta ga gwamnatin Najeriya a yakin da take yi da ta’addanci a kasar.
Ya ce, tunda OIC ta fitar da matsaya cewa ayyukan Boko Haram sun saba wa Musulunci tana bukatar a ayyana Boko Haram a matsayin kungiyar ’yan ta’adda da ayyukanta suka saba wa Musulunci. Sai ya yi alkawarin cewa a shirye kungiyar OIC take wajen taimaka wa Najeriya wajen yaki da ta’addanci, inda ya ce idan aka ba ta dama kungiyar za ta shirya taron tattaunawa a tsakanin mabiya addinai a kasar nan, domin tattauna gaskiyar da’awar da ’yan ta’addan ke yi tare da nuna yadda ya kamata mabiya addinai za su zauna lafiya da juna.
Ya ce a matsayin Najeriya ta wakiliya a kungiyar, wajibi ne OIC ta nuna damuwa kan yadda ake fakewa da Musulunci ana yin abubuwan da suka saba wa addinin.  
Ministan Harkokin Waje, Ambasada Aminu Wali ya ce Najeriya ta riga ta bukaci neman tallafi daga kowane bangare, kuma kasar za ta nemi tallafin OIC domin wadanda aka sanya su gudun hijira a cikin gida daga garuruwansu.