Ojukwu da rawar da ya taka a juyin mulkin 1966 (II)
Bisa la’akari da wadannan tabbatattun bayanai, wa ya jefa Ibo a cikin mawuyacin hali, idan ba Ojukwu ba?
Kamar yadda muka fara wannan maudu’i a makon jiya, yau cikin nufin Allah za mu dora daga inda muka tsaya.
Munanan abubuwa sun ci gaba da faruwa a Arewa, kamar kama daliban Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ’yan kabilar Ibo da aka yi da makamai suka ce an aiko musu ne daga gida don su far wa ’yan Arewa.
Wato dai yakin an shirya ta yadda za a far wa ’yan Arewa ta kowane janibi, domin daga zarar an ce an far wa dalibai a cikin jami’a shi ke nan makaranta ta hautsine.
A yayin wannan bincike har ila yau, aka kara kama wani dan kabilar Ibo da bam zai jefa a ‘Lugard Hall’ wato Majalisar Dokoki ta Arewa, a daidai lokacin da shugabannin Arewa suke gudanar da taro a wajen.
Haka an sake kama wasu Ibo su ma da bam za su sa a katafaren otal din nan da ake kira ‘Hamdala Hotel’ da babbar gadar Barnawa/ Narayi.
Irin wannan mummunan nufi da hikidi da muguwar niyya ta Ibo sun nuna tsangwama da nuna tsana da muguwar kiyayyar da Ibo ke nuna wa Arewa da kuma mutanenta, duk da cewar dubban Ibo na cikin kusan dukkan kasuwannin Arewa suna kasuwanci.
Wancan tsaro da Allah Ya bai wa mutanen Arewa ya firgita Ibo sosai, ganin duk yunkurinsu bai kai ga gaci ba, Allah Yana tona asirinsu.
Daga nan ne, sai suka fara gudu zuwa yankunansu na Kudu maso Gabas, suna yin sansani watakila don tsoro ko domin sake dabarun yadda za su fito wa mutanen Arewa.
Ganin haka, suka fara far wa mutanen Arewa da ke warwatse a yankin Kudu maso Gabas suna sana’ar fawa da sauran dangin kasuwanci.
Haka aka kama fafarar ’yan Arewa daga kusan dukkan yankunansu.
Ganin haka sai ’yan Arewa suka fara rarakar su gida can Kudu.
Wasu kuma ba korar su aka yi ba, suna tunanin sojojin Ibo za su kara sabon juyin mulki ne tunda an kashe Ironsi, don haka bai kamata su kasance a Arewa ba.
Wasu kuma na zargin Arewa da shigo da makamai daga kasashen Larabawa don yin jihadi.
Wasu kuma jin haushi suke don ware wani sashi a bangaren shari’a aka ce na Musulmi ne, wannan na cikin abubuwan da har gobe Ibo suke nuna kiyayya da jin haushin mutanen Arewa musamman Musulmi a kansa.
Haka kuma, wasu manyan ayyukan ta’addanci da manyansu suka yi da suka san ba za a hakura ba, sun taimaka.
Misali bayan kashe Laftanar Kanar Largema, janyo gawarsa suka yi kamar mushe daga benen Ikoyi Hotel da ke Legas.
Sa Abubakar Tafawa Balewa kuma giyar burkutu Manjo Donatus Okafor ya ba shi, suka tilasta masa kwankwadarta, ya ce masa idan ya sha za su kyale shi. Da sauran cin zarafi da suka rika yi wa manyan Arewa a lokacin da suka kama su kafin su karkashe su, kisan wulakanci da tozartawa.
Wadannan ma sun taimaka ga hijirar Ibo daga yankunan Arewa zuwa Kudu.
Yayin da ake wadancan guje-guje daga Arewa zuwa Kudu, sannan daga Kudu zuwa Arewa, ’yan Arewa na sayen kadarorin Ibo da suke guduwa, amma a yankinsu na Kudu babu wani mai sayen komai na dan Arewa.
Sai dai ka dauko abin da za ka iya dauka, ka bar sauran abin da ba za ka iya jigilarsa zuwa gida Arewa ba kamar gida ko fili, saboda haka ya zama ganima gare su.
Haka suka wawashe manyan kadarorin da ’yan Arewa suka mallaka a yankunansu.
Da rikici ya lafa, mutane suka fara komawa wuraren kasuwanci da sana’o’insu, har kudin hayar gida da shaguna wasu Ibo sun tarar an tara masu a Arewa, saboda mutumin Arewa bai gaji zalunci da cin amana ba.
Hakan ta bai wa jagoran ’yan aware wato Ojukwu, Gwamnan Jihar Gabas, wanda ya rasu a ranar 11 ga Nuwanban 2011 aka rufe shi a watan Mayun 2012 bayan gagarumin biki don zolayar ’yan Arewa bisa jagorancin Shugaban kasa Goodluck Jonathan da kuma damar da yake nema ta samun shiga wajen Ibo, dama ya yi ta zuzuta lamarin, inda yake cewa Ibo duk inda suke kada su yi tsammanin samun kariya ga rayuka da dukiyoyinsu in dai ba a Gabas suke ba, wato yana tunzura Ibo a kan duk su taru su su yi sansani.
Ma’ana su koma Gabas can ne za a kare mutuncinsu.
Sai suka manta cewa yankin da yake zagi nan aka haife shi (shi da Azikwe).
Ya yi ta kalamai irin na Nzeogwu cewa sun yi juyi ne don kabilanci da wariyar da ake nunawa ga sauran ’yan kasa musamman su Ibo.
Alhali sun biye wa son zuciya ne suka rabe da kabilanci.
Domin duk wanda ya binciki tarihi zai fahimci Nzeogwu, Okafor da Ironsi sun samu tagomashi ne daga mutanen Arewa, suka zama abin da suka zama.
Shi kansa Ironsi bai cancanci zama shugaban sojoji ba a lokacin aka nada shi, don kuwa Zakariyya Maimalari ne ya dace da mukamin, amma saboda kara irin ta mutumin Arewa ta sa Tafawa Balewa ya damka wa Ironsi wannan mukami, duk saboda a zauna lafiya a samu kyakkyawar zamantakewa tsakaninmu da su.
Wannan abin da ya faru sai da ya so ya jawo baraka a tsakanin ’yan Arewa domin su Sardauna sun ja hankalin Tafawa Balewa kan illar damka wannan muhimmin mukami ga Ironsi.
Sardauna ya gaya wa Balewa cewa shi ke nan ka kashe mu! Haka kuwa aka yi, kamar ya san abin da zai faru da su har da Balewan.
A 1965 kididdiga ta nuna cewa kashi 4 cikin 100 na mutanen Arewa ke rike da manyan mukaman Gwamnatin Tarayya.
Zuwa 1966 kuma sama da kashi 25 cikin 100 na manyan ma’aikatan gwamnati a Jihar Arewa mutanen Kudu ne, mafiya rinjayensu ’yan kabilar Ibo.
Ba a maganar kananan ma’aikata, ba mu iya rike namu ba da har wani zai ce mun karbe masa nasa.
Bisa la’akari da wadannan tabbatattun bayanai, wa ya jefa Ibo a cikin mawuyacin hali, idan ba Ojukwu ba?
Amma saboda rashin sanin tarihi da kuma bibiyar abin da ya faru jiya, har wani sakarai zai zo ya hure wa matasan Ibo kunne su bi shi ido rufe?
Wani tsohon Kwamishinan Sadarwa a Jihar Anambara zamanin Gwamnatin Chinwoke Mbadiniju mai suna Prince Emeka Nkwocha ya bayyana Ojukwu kamar haka: “Ojukwu mutum ne mai son rikici da son a sani tun yana matashi.
“Mutum ne da ya tashi cikin gata a daidai lokacin da ’yan Najeriya ke fama da talauci da tsananin wahala, hakan ya yi tasiri a rayuwarsa.
“Don haka ya kasance dan agwagwa, wanda ba ya bi sai dai a bi shi.
“Sojojin Ibo da yawa sun zargi Ojukwu da kin taimakon Nzeogwu don bai ayyana shi a matsayin shugaban gwamnati ba, don haka ya tafi Biyafra don jagorantar ’yan tawaye…” Mujallar The Week 11 ga Oktoba, 2004.