Ojulari ya inganta harkokin NNPC — PNGI
NNPC ya samu nasarar ƙara yawan samar da ɗanyen mai zuwa kusan ganga 355,000 a kowace rana a shekarar 2025.
Ƙungiyar Progressive Next Generation Initiative (PNGI) ta yaba wa Shugaban Rukunin Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC), Bashir Bayo Ojulari, bisa abin da ta kira ingantattun sauye-sauyen da ya kawo a kamfanin tun bayan kama aikinsa a ranar 2 ga Afrilun 2025.
A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a ranar Litinin, 26 ga Janairu, 2026, mai ɗauke da sa hannun shugabanta, Hon. Jeffery Omoh Ozemegwa.
PNGI ta ce shugabancin Ojulari, duk da ɗan gajeren lokacin da ya shafe, ya sabunta kyakkyawan fatan da ake yi wa harkar makamashi musamman man fetur da gas, tare da shimfiɗa tubalin gaskiya, aiki tuƙuru da ci gaban ƙasa.
- Jirgin sojojin sama ya kashe mamoma 2 ‘bisa kuskure’ a ƙauyen Neja
- Malamin firamare ya samu kyautar N50m, mota da gida
Ƙungiyar ta bayyana Ojulari a matsayin shugaba mai kishin ƙasa da hangen nesa, wanda ya fara aiwatar da sauye-sauyen da suka haɗa da sake fasalin manyan shugabannin kamfanin, raba ayyuka yadda ya kamata da kuma sanya ido kan sakamako, domin tabbatar da ingantaccen aiki a NNPC.
PNGI ta ce daga cikin muhimman matakan da Ojulari ya fara akwai ƙarfafa haɗin gwiwa a fannoni daban-daban na harkar mai da gas, ciki har da bincike da haƙo mai, tattarawa da jigila, da kuma tacewa da rarrabawa, lamarin da ya taimaka wajen inganta ayyukan kamfanin.
A cewar ƙungiyar, “NNPC ya samu nasarar ƙara yawan samar da ɗanyen mai zuwa kusan ganga 355,000 a kowace rana a shekarar 2025, sakamakon wasu muhimman ayyuka da suka haɗa da fara samar da mai daga Modu field, gyaran bututun Soku pipeline corridor, da kuma fara aiki a Akpo West.”
Sanarwar ta ƙara da cewa “shugabancin Ojulari ya mayar da hankali kan tsare-tsaren dogon zango, inda aka sa gaba samar da ganga miliyan biyu na ɗanyen mai a kowace rana nan da 2027, da kuma ganga miliyan uku a 2030, ta hanyar zuba jari mai tsari da kare kadarorin ƙasa.”
PNGI ta ce “Ojulari ya dawo da fitar da rahotannin kuɗi da na ayyuka kowane wata, tare da aiwatar da sabbin ka’idojin rabon iko da rage almubazzaranci, domin mayar da NNPC kamfani mai tafiya bisa tsarin kasuwanci.
Ƙungiyar ta kuma yaba da matakan bunƙasa ma’aikata da Ojulari ya ɗauka, ciki har da kyautata walwalarsu da ɗaukar sabbin matasa ƙwararru, domin gina shugabannin fannin makamashi na gaba.
PNGI ta ce waɗannan sauye-sauyen sun ƙara yawan gudunmawar da NNPC ke bai wa Asusun Tarayya, tare da ƙarfafa tattalin arzikin kamfanin da rawar da yake takawa wajen bunƙasa ƙasar.
A ƙarshe, ƙungiyar ta bayyana Ojulari a matsayin abin koyi ga matasan Nijeriya wajen nagartaccen shugabanci, tana mai cewa shugabancinsa ya fara ɗora NNPC a turbar da ta dace da sauyin da duniya ke ciki a harkokin makamashi.