Okocha ya zama Gwarzon dan kwallon Bolton

Tsohon dan kwallon Najeriya da kuma kulob din Bolton Wanderers na Ingilla Jay-Jay Okocha ya zama Gwarzon dan kwallon kulob din a wani zabe da magoya bayan kungiyar suka yi a karshen makon jiya. Magoya bayan sun zabi Jay-Jay Okocha ne a matsayin Gwarzon dan kwallon kulob din da aka taba yi a lokacin bikin […]

Okocha ya zama Gwarzon dan kwallon Bolton

Tsohon dan kwallon Najeriya da kuma kulob din Bolton Wanderers na Ingilla Jay-Jay Okocha ya zama Gwarzon dan kwallon kulob din a wani zabe da magoya bayan kungiyar suka yi a karshen makon jiya.

Magoya bayan sun zabi Jay-Jay Okocha ne a matsayin Gwarzon dan kwallon kulob din da aka taba yi a lokacin bikin cika shekara 20 da fara amfani da katafaren filin wasansu mai suna Reebok Stadium da aka gina tun a shekarar 1997.  Sai dai a shekarar 2014 ne wani kamfani mai suna Macron ya kulla yarjejeniyar canza sunan filin wasan zuwa na Macron Stadium maimakon Reebok a wannan shekara (2017).

A lokacin bikin canza sunan filin wasan ne magoya bayan kulob din suka gudanar da zaben don zakulo Gwarzon dan kwallon kulob din tun daga kafuwarsu kawo yanzu inda Jay-Jay Okocha ya samu rinjayen kuri’u.

Okocha dai ya fafata a zaben ne da tsofaffin ’yan kwallon kulob din irin su Iban Campo na Sifen da Youri Diorkaeff na Faransa kafin ya zama Gwarzon.