Okpebholo na APC ya lashe zaɓen Gwamnan Edo

Mulki ya sake dawowa hannun jam’iyyar APC bayan rashin nasara da ta yi a shekarar 2020.

Okpebholo na APC ya lashe zaɓen Gwamnan Edo

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta ayyana Monday Okpebholo na jam’iyyar APC, a matsayin wanda ya lashe zaɓen Gwamnan Jihar Edo da aka gudanar ranar Asabar.

Okpebholo, mai shekara 54, ya samu ƙuri’u 291,667, inda ya doke Asue Ighodalo na jam’iyyar PDP, wanda ya samu ƙuri’u 247,274 da kuma ɗan takarar jam’iyyar LP, Olumide Akpata, wanda ya zo na uku da ƙuri’u 22,761.

Sauran ’yan takarar guda 14 da suka shiga zaɓen ba su samu ƙuri’u kamar na waɗannan jam’iyyun uku ba.

Da misalin ƙarfe 9:27 na ranar Lahadi, jami’in tattara sakamakon zaɓe na INEC, Farfesa Faruk Kuta, ya ayyana Okpebholo a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen gwamnan.

Sanarwar ta yi magoya bayan APC a cibiyar tattara sakamakon zaɓen da ke Benin daɗi.

Farfesa Kuta, shi ne Shugaban Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Minna, a Jihar Neja, kuma ya sanar da nasarar Okpebholo bayan hutun da INEC ta yi yayin tattara sakamakon zaɓen.

Ɗan takarar APC, ya yi nasara a ƙananan hukumomi sama da 10 daga cikin 18 da ke jihar, yayin da ɗan takarar PDP ya lashe sauran ƙananan hukumomin.

APC ta samu rinjaye a sassa biyu daga cikin uku na manyan yankunan Sanata a jihar.

Okpebholo, Sanatan Edo ta Tsakiya, ya samu goyon baya mai ƙarfi a yankinsa, tare da haɗin gwiwar tsohon gwamnan jihar kuma Sanata ma ci a yanzu, Adams Oshiomhole.

Har ila yau, Okpebholo ya samu goyon bayan abokin takararsa, Dennis Idahosa da tsohon mataimakin gwamnan jihar, Phillip Shaibu.

Wannan nasarar na nufin Okpebholo ya kusa cimma burinsa na zama gwamnan jihar, tare da dawo da mulki hannun jam’iyyar APC a jihar.

APC ta rasa mulki a Jihar Edo a shekarar 2020, lokacin da gwamna mai ci, Godwin Obaseki, ya fice daga jam’iyyar APC ya koma PDP saboda rikicin cikin gida.

Obaseki, ya lashe wa’adi na biyu a ƙarƙashin jam’iyyar PDP.

Yayin da wa’adinsa zai ƙare a watan Nuwamba, 2024, Obaseki ya goyi bayan takarar Ighodalo tare da ɗaukar nauyinsa, yayin da Oshiomhole ya kasance babban jigo a takarar Okpebholo.

Zanga-zanga ta ɓarke kan zargin tafka maguɗi

Duk da cewa an ayyana Okpebholo a matsayin wanda ya yi nasara, magoya bayan jam’iyyad PDP sun gudanar da zanga-zanga kan zargin cewa an yi maguɗi wajen tattara sakamakon zaɓen.

Magoya bayan PDP gudanar da zanga-zangar a wasu sassan babban birnin jihar da kuma cibiyar tattara sakamakon INEC, wadda jami’an tsaro suka tsaurara matakan tsaro.

Gwamna Obaseki, ya je cibiyar tattara sakamakon zaɓen domin nuna rashin jin daɗinsa game da hana wakilan PDP shiga wajen, amma jami’an tsaro suka fitar da shi daga cibiyar.

Wakilin PDP a cibiyar, Tony Iyoha, ya nemi a soke zaɓen gaba ɗaya saboda zargin tafka maguɗi.

Kazalika, shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Anthony Aziegbemi, ya bayyana cewa lambar ƙuri’un da ke kan fom ɗin EC8 ba su yi daidai da waɗanda ke kan na’urar IReV ta INEC ba.

Ƙungiyar Gwamnonin PDP ta nemi hukumar zaɓe ta girmama zaɓin al’ummar Jihar Edo, ta hanyar barin abin da suka zaɓa.

Gwamnonin PDP, ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, sun soki wasu daga cikin sakamakon da aka bayyana, wanda suka nuna cewa ba su yi daidai da waɗanda ke kan na’urar IReV ba.

A cewar INEC, mutum 2,249,780 masu katin zaɓe ne suka zaɓi wanda zai gaji Obaseki a ranar Asabar, 21 ga watan Satumba, 2024.

Jihar Edo na daga cikin jihohin takwas da ake gudanar da zaɓen gwamna a lokacin da ba kakar zaɓe ba saboda sakamakon sauyin lokaci da hukuncin kotu ya yi a baya.

Sauran jihohin sun haɗa da Anambra, Bayelsa, Ekiti, Imo, Kogi, Osun da kuma Jihar Ondo.

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato

Yadda gobara ta ƙone kasuwar babura a Zamfara

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra