Oktoba: Yadda Kanawa suka yi watsi da batun zanga-zanga

Mutane da dama sun tafi harkokinsu kamar yadda suka saba tare da watsi da batun zanga-zangar.

Oktoba: Yadda Kanawa suka yi watsi da batun zanga-zanga

Jama’ar Jihar Kano, sun yi watsi da zanga-zangar da aka shirya gudanarwa a faɗin ƙasar nan, tare da ci gaba da al’amuransu na yau da kullum.

Zanga-zangar da aka shirya yi a ranar 1 ga watan Oktoba, 2024, wanda aka yi wa lakabi da “FearlessInOctober”, an yaɗa ta a shafukan sada zumunta kimanin watanni biyu bayan zanga-zangar #EndBadGovernance da aka yi a watan Agusta.

Dukkanin zanga-zangar suna da jigo ɗaya, inda matasa masu suke nuna fushinsu da buƙatar a dawo da tallafin mai da aka cire da kuma ƙara farashin wutar lantarki.

A Kano, wakilinmu ya ruwaito cewa duk da cewa wannan rana ta kasance hutu, mutane da yawa sun zaɓi zama a gida.

Duk da haka, wasu sun fita don gudanar da kasuwancinsu na yau da kullum.

Manyan hanyoyi a jihar sun kasance shuru babu kowa, sannan garin ya kasance fayau babu cunkoso.

A gefe guda kuma, ‘yan tsirarun shaguna da masu gudanar da kasuwanci a gefen hanya sun buɗe.

Manyan kasuwanni kamar Kwari, Sabon Gari, Singa da Kurmi sun kasance a buɗe, inda aka samu ɗaiɗaikun shaguna a rufe.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wani bayani kan zanga-zangar da ke gudana a ko ina faɗin jihar.

An ƙwace kwantainoni 54 mallakin Emefiele

Fulawa da dabbobin Fadar Shugaban Ƙasa za su ci N125m a 2025

Za a rataye shi saboda kisan jariri

Kirsimeti: Gwamnati ta fara jigilar fasinjoji kyauta a jirgin ƙasa