Oliseh ne sabon kocin Eagles
A shekaranjiya Laraba Hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ta bayar da sanarwar daukar Sunday Oliseh a matsayin sabon kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles.. Sai dai hukumar ta ce Oliseh zai yi aiki ne da wani Bature a matsayin mataimakinsa da za ta dauka nan gaba kadan don ganin sun farfado da martabar […]
A shekaranjiya Laraba Hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ta bayar da sanarwar daukar Sunday Oliseh a matsayin sabon kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles..
Sai dai hukumar ta ce Oliseh zai yi aiki ne da wani Bature a matsayin mataimakinsa da za ta dauka nan gaba kadan don ganin sun farfado da martabar kungiyar.
Hukumar ta ce tana da yakinin Oliseh yana da kwarewar da zai taimaki kungiyar wajen samun nasara.
Shugaban kwamitin da ke alhakin tantancewa da kuma daukar koci a Hukumar NFF Cif Felid Anyansi ne ya sanar da haka a lokacin da yake hira da manema labarai.
“Mun gabatar da bukatarmu ga Olieh kuma ya amince da kwantaragin da muka gabatar masa, don haka muna sa ran nan da ’yan kwanakin kadan zai sanya hannu a kwantaragin don ya kasance sabon Kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles”, inji Anyansi.
Oliseh wanda zai yi aiki da wani Bature a matsayin mai taimaka masa, ana sa ran za su hada karfi wajen farfado da martabar kwallo a Najeriya tun daga matakin yara.
Shugaban ya kara da cewa akwai tsarin da Hukumar NFF ta yi don a rika ilimantar da kococin da ke cikin gida daga lokaci zuwa lokaci don su ma su goge.
A nasa bangaren, Shugaban Hukumar NFF, Amaju Pinnick ya bayyana Sunday Oliseh a matsayin kwararre wanda zai farfado da harkar kwallo a kasar nan. Ya ce Oliseh mutum ne da ake girmama shi a tsakanin ’yan wasa da kuma jami’an hukumar ta NFF don haka ba zai samu matsala a wajen gudanar da aikinsa ba. “Mutum ne da ya san abin da yake yi, kuma ya ba mu shawarwari a kan hanyoyin da suka kamata mu bi don mu samu nasara don haka na yaba da wannan matsayi da aka ba shi na kocin Super Eagles”.
Oliseh dan shekara 40, a yanzu shi ne jami’in tuntuba a Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA inda yake ba hukumar shawarwari a kan kococin da suka fi nuna kwazo a sassan duniya inda hukumar kan gayyace su don karrama su.
Salisu Yusuf wanda aka ba shi rikon Super Eagles kafin a nada sabon koci yana daga cikin wadanda za su cigaba da aiki da Oliseh kamar yadda hukumar ta sanar.
Sunday Oliseh dai bai taba horar da wata babbar kungiyar kwallon kafa a ciki da wajen Najeriya ba, al’amarin da ya sa wasu ke ganin da wuya kocin ya isa samun nasara, tun da ba shi da kwarewa a kan harkar horarwa.